2022: Tattalin arzikin Nijeriya zai habaka -Bankin Duniya

Daga Muhmud Gambo Sani
Bankin Duniya ya yi hasashen samun habakar tattalin arzikin Nijeriya da akalla kashi 2.5 cikin 100 a shekarar 2022. Alkaluman da bankin ya fitar kan hasashen tattalin arzikin kasashe, ya ce tattalin arzikin Nijeriyar zai rinka habaka shekara bayan shekara wanda ke da nasaba da tashin farashin man fetur da kuma kudaden da kasar ke samu a bangaren sadarwa da hukumomin kudi.
Nijeriyar ita ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka wadda ta dogara da man fetur wajen samun kudaden shiga, alkaluman da Bankin na Duniya ya fitar ya nuna cewa, bayan samun karuwar tattalin arziki. Wadansu daga cikin dalilan da za su taimaka wa tattalin arzikin Nijeriya a cewar bankin, akwai matakin kungiyar OPEC na rage yawan man da manyan kasashe masu arzikin man fetur ke fitarwa da kuma wadansu sababbin tsare-tsaren da za su taimaka wa kananun kasashen kungiyar.
Sai dai duk da habakar tattalin arzikin, kamar yadda bayanan bankin suka nuna, Nijeriyar za ta ci gaba da fuskantar matsalolin da annobar korona ta haddasa wa bangaren samar da ayyukan yi.
Alkaluman bankin sun ce, yanayin samar da ayyukan yi zai ci gaba da tafiyar hawainiya a sassan Nijeriyar, haka zalika zai dauki lokaci gabanin daidaituwar farashin kayayyaki musamman na abinci.
Alkaluman bankin sun nuna cewa, duk da habakar tattalin arzikin har zuwa 2023 al’amura ba za su koma kamar yadda su ke kafin korona ba.