2023: APC za ta lashe zabe a dukkan matakai – Zainawa

apc

Alamar APC

Tura wannan Sakon

Labarai Daga Salihu S. Gezawa

An bayyana jam’iyyar APC a matsayin, jam’iyyar da za ta lashe zaben 2023 tun daga kan shugaban kasa da gwamnan Kano da sanatoci da ‘yan majalisun tarayya da na johohi, cikin yardar Allah. Shugaban karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano, Alhaji Hudu Usman Zainawa ne ya yi bayanin a zantarwarsa da manema labarai, in da ya ce, babu tantama a jihar Kano, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ne amsa, domin shi ne dan takara mafi dacewa da cancanta da rike mukamin gwamna, kasancewar gogagge, mai hakuri da juriya da kuma kishin ci gaban jihar Kano.

Hudu Zainawa ya ce, idan aka koma baya za a ga tarihin Gawuna lokacin da ya shugabanci karamar hukumar Nasarawa, inda ya yi rawar gani tare da kyautata rayuwar al’ummar karamar hukumar, tare da kyautatawa ma’aikatan karamar hukumar. Zainawa ya ce, haka kuma idan aka kalli Murtala Sule Garo, wanda shi ma yake cewa, an ajiye kwarya a gurbinta.

Domin tarihin siyasar jihar Kano ba zai cika ba, sai san sawo Galadiman Garo, wanda ya ceto Kano a zaben 2019. Zainawa ya ci gaba da cewa, Murtala Sule Garo, tsohon shugaban karamar Hukuma ne a Kabo, kuma kwamishinan kananan hukumomi da ya taka rawar gani wajen fitar da kananan hukumomi daga kangi. Daya juya ga karamar hukumar Gezawa, Hudu Zainawa ya ce, yana aiki iya kokarin domin ciyar da karamar hukumar goba ta bangarorin ilimi, inda ya yi gyaran makarantun firamare masu yawan gaske daga sassa dabandaban na karamar hukumar, baya inganta lafiya da noma da kiwo tare da inganta rayuwar mata da matasa da masu rauni.

Zainawa ya ce, shugabansa, shugabanci ne mai kofa a bude babu dagawa ko girman kai illa, sauraron jama’a mutuntasu tare da kyautata mu’amala wanda shi ne babban jigon shugabanci. Daga nan ya gode wa al’umma karamar hukumar kan goyon bayan da suke ba shi tare da kira kan a ci gaba da addu’o’i dan samun zaman lafiya a Kano da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *