2023: Gawuna/Garo a kan mizani

2023: Gawuna/Garo a kan mizani

Gawuna/Garo a kan mizani

Tura wannan Sakon

Daga Aminu Dahiru

Akalla yau saura wata 7 a yi zaben gwamnoni, zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar tarayya zai gudana cikin ikon Allah 25 ga Faburairu, a yayin da zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jiha zai gudana 11 ga Maris na shekarar 2023. Har izuwa yanzu dai ba a kada gangar siyasa ba, a hukumance domin bai wa ‘yan takarkaru damar tallata hajarsu.

Duk da haka akwai wata tambaya mai matukar muhimmanci da ke tsimayin amsa daga wajen Kanawa.

Tambaya ita ce: waya ya cancanta da ya ci gaba da gudanar da al’amuran jihar Kano mai albarka bayan wa’adin mulkin Ganduje ya kare a shekarar 2023? Akwai abubuwa da yakamata a yi la’akari da su kafin bayar da amsa. Duk wani akili wanda ya kai shekarun zabe ya kamata ya fahimci daga inda ake kuma ina za a je.

Ya kamata a yi duba na tsanaki kan nasarori da gwamnatin jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC ta samu a cikin shekaru 7 da wadansu watanni da suka gabata da matakin da jihar take kafin wannan lokaci da kuma yanzu.

Bayan haka akwai bukatar dora kowane dan takara a mizani domin fahimtar irin amfani da yake da shi ga al’ummar jiha, da kudirekudire da yake da su domin ci gaba da inganta rayuwar Kanawa musamman matasa da mata. Zaben 2023, zabe ne na goyan bayan ci gaba ko akasin haka.

Zabe ne da zai mayar da hankali wajen mu’amalar dan takara da yadda yake jibintar al’amuran al’ummarsa da biyyarsa ga shugabanni da kuma irin kauna da yake da ita ga wannan jihar da ake wa lakabi da cibiyar kasuwanci. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi hangen nesa da zurfin tunanin da ya zabawa al’ummar jihar mataimakinsa, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishina na kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin dan takarar gwamna da kuma mataimakinsa a kakar zabe mai zuwa a karkashin jam’iyyar APC.

Dokta Nasiru Yusuf Gawuna gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kuma dan siyasa wanda yake da halin dattako. Ya yi shugaban karamar hukuma har sau biyu, tsohon kwamishina ne. Har ila yau, kuma mataimakin gwamna ne babu wani lungu ko sako na gwamnati da zai shige masa duhu. Juriya da hakuri da hangen nesa da wadatar zuci su ne kalmomin da za ka iya siffanta Gawuna da su.

Gogewarsa a fannin gudanarwa da irin gudumawar da ya bayar ga wannan jiha tun lokacin da ya zama mataimakin gwamna manuniya ce cewa, babu wani wanda ya fi cancanta da ya zama gwamna a shekarar 2023 fiye da wannan bawan Allah.

Alhaji Murtala Sule Garo tsohon kwamishinan kananan hukumomi ne na wannan jiha, matakin da ya rike tsawon shekaru 7 da wadansu watanni. Garo cikakken jagora ne, jagaba ne a wajen fannin siyasar jihar, ya gina matasa Allah ne kawai ya san adadin matasa da mata da ya tallafa wa wanda a yanzu haka suna tsaye a kan kafafuwansu.

Ana masa lakabi da Kwamande ne domin jajircewar sa wajen ganin an yi abin da ya dace a lokacin da ya dace, babban burinsa shi ne gina matasan jihar birni da kauye.

Tabbas idan ka dora Dokta Nasiru Yusuf Gawuna Gawuna da Murtala Suke Garo a kan mizani za su rinjayin duk wadansu ‘yan takarkaru.

Dalili, kuwa shi ne, babbar manufarsu ita ce, gina al’ummar jihar, musamman matasan ta da mata domin ci gaba mai dorewa a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *