2023: Muhammad Garba, wakilci nagari

Muhammad Garba

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad Suleiman, Kano

Jihar Kano ta dade ba ta yi kwamnishinan yada labarai kamar Muhammad Garba, ko da yake kwarya ce aka sa ta a gurbin ta. Zaban Kwamare Muhammad Garba a matsayin kwamishina na yada labarai da harkokin cikin gida da gwamnan ya yi, ya yi ne domin Malam Garba ya san aikinsa, kuma dan jarida ne mai hangen nesa da kuma rikon amana.

Ya rike shugabancin kungiyar ‘yan jarida ta kasa har karo biyu, yana da alaka da ‘yan jaridu a fadin kasar nan mutum mai saukin kai da son abokan aikinsa a duk inda ya samu kansa.

Kwamare Muhammad Garba ya kawo ci gaba a zamansa kwamishina yada labarai a Kano da kuma kare muradan gwamnatin jihar Kano a ko’ina ya samu damar yin haka. Ganin irin jajircewarsa da kishin al’umma ba nuna bambanci matasa da iyayen karamar hukumar birni da kewaye suke kira da ya zo ya wakilcesu a majalisar tarayya kasa, domin Hausawana cewa rikon amana sai dan kunya” Muhammad Garba ya canci yabo da kuma rike amanar da Ganduje ya saura masa tun daga zango na farko zuwa zango na biyu.

Karamar hukumar Birni tana neman mutum da ya san aikinsa, kuma haziki mai hangen nesa, mutum da zai tsaya ya turance duk wani kalubale na wakilci jama’ar da zai jagoranta. Kwamred Muhammad Garba Abuja ba bakuwarsa ba ce, ba lugun da ba zai shiga ba domin ganin ya kwato wa jama’arsa hakkinsu a gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *