A 2021: Mun Sami Nasarar Warware Matsaloli Fiye da 3000 -Qaribu Kabara

Tura wannan Sakon

Daga Rabi’u Sunusi Katsina

Kimanin matsaloli fiye da dubu 3600 ne gamayyar qungiyar kare haqqin xan’adam ta samu nasarar warwarewa a shekarar 2021 da ta gabata a jihar Kano.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban daraktan gamayyar qungiyoyin kare haqqin xan’adam, Kwamred Qaribu Yahaya Lawal Kabara ne ya bayyana haka ga wakilin Albishir a wata ziyarar aiki da ya kai wa daraktan a ofishinsa makon jiya.

Daraktan kuma bayyana cewa, aikin qungiyar ne ta tabbatar an samu daidaito da masalaha tare zaman lafiya a cikin al’ummar jihar Kano dama qasa baki xaya.

Haka kuma ya tabbatar da samun qorafe-qorafe fiye da dubu 3 a shekarar da ta gabata da suka haxa da matsalar zamantakewar aure fiye da dubu 1000, sai matsalar ‘yan-kasuwa da maqwabtaka tare da matsalar vatanci fiye da dubu.

Qaribu Yahaya ya bayyana qungiyar a matsayin wadda take qoqari wajen ganin an samar da zaman lafiya da daidaito ga matsalolin al’umma tare da bai wa mai haqqi haqqinsa da kowane sashe ko qabila. Sannan ya ce, babbar nasara a nan ita ce, daidaiton ma’aurata na xaya daga cikin nasarorin da ofishinsu ya samu ta hanyar aika masu matsalar ga jami’an tsaro kama daga ‘yan-sandada hukumar Hisbah da vangaren ‘yan banga da sauran sashen da ya danganci kotu da makamantan su.

Qaribu wanda shi ne jagoran qungiyar tsawon shekaru 4, ya ce, ba su da wani buri ko fata da ya wuce ganin koda yaushe an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’umma kuma koda yaushe suna maraba da wanda zai taimaka wajen samo hanyar da za’a magance matsalolina cikin al’umma.

 Haka zalika ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar fahimata da gwamnati da hukumar kare haqqin xan’adam ta su, ya ce, vangaren kotu ma na turo masu waxansu kyasa kyasai da hukumar Hisbah da sauransu, yayin da za su gabatar da aiki kan matsalar da suka aike masu za ka ga nasara ta fito, nan ta ke kuma su miqa wa sashen da ya ba su damar gudanar da bincike da sulhu ga al’umma walau gwamnati ko jami’an tsaro cikin nasara.

Haka kuma daraktan ya ci gaba da cewa, a waxansu lokutan masu unguwanni da dagattai da hakimai sukan tura masu kyes da samar da masalaha ga al’umma kuma cikin yardar Allah a kan yi nasara, domin sai dai wanda ya voye gaskiya a cikin zuciyar sa sannan ake samun akasin haka, kuma ya ce, sukan tara mai qara da wanda ake qara domin jin ta kowane sashe da nemo hanyoyin magance matsalolin.

Shugaban gamayyar qungiyoyin ya kuma buqaci shugabannin qananan hukumomi na jihar Kano da su qoqarta yin taron wayar wa da mazauna karkara kai, domin rashin ilimi na taka rawar gani wajen fuskantar waxannan matsaloli da ake fama da su musamman a zamantakewar.

Daga qarshe, ya bayyana irin godiyar sa ga sauran abokan aikinsa bisa yadda suke bayar da gudunmuwa domin ganin sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *