A 2023: Atiku ya fi dacewa ya zama shugaban kasa -Danwawu Fagge

‘Yan Nijeriya, a zabi Atiku Abubakar
Alhussain daga Kano
Babu shakka dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar shi ne ya fi dacewa ya zama shugaban kasa a zaben da ke tafe.
Bayanin ya fito ne daga bakin daya daga cikin daraktocin yakin neman zaben, Atiku Abubakar dake jihar Kano, Alhaji Hamisu Danwawu Fagge, alokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa da ke Kano.
Alhaji Hamisu Danwawu Fagge, ya ce, Atiku Abubakar kowa ya san cewa, ya goge sosai a kan fannin siyasa da kuma sanin halin da kasar nan da ke ciki, kuna har ila yau, za kuma a samu daidaito tsakanin kabilun kasar nan ba tare da yawan samun rigingimu tsakanin su ba.
Babban abin da dantakarar yake bukata in ji Hamisu Danwawu Fagge daga wurin masoya da magoya baya ita ce, addu’a da kuma goyon baya ranar zabe kuma su tabbatar sun zabi jam’iyyar PDP tun daga sama har kasa.
Ya ce, alamu sun nuna cewa, PDP tana kara samun karbuwa sosai domin har yanzu shiga ake yi, kuma al’umma canji suke bukata.
Hamisu Danwawu Fagge, shi ne daraktan yakin neman zaben Sadik Aminu Wali a matsayin gwamnan jihar Kano, a jam’iyyar PDP ya ce, da yardar Allah shi zai lashe zaben gwamnan jihar a 2023, matashi ne da ya iya siyasa ya kuma iya mu’amala sannan kuma zai kawo wa jihar ci gaba ta fannonin da dama.
Dan takarar yana da tsare-tsare masu kyau a kananan hukumomin jihar 44, kuma shi ne ya lashe zaben fitar da gwani da aka kammala kwanakin baya a jam’iyyar PDP.
Danwawu ya yi amfani da wannan dama da kira al’ummar jihar Kano maza da mata cewa, ya zama wajibi ga duk wanda bai karbi katin zabe ba, ya hanzarta karbar domin da shi ne mutum yake zaben shugaban da yake so ranar zabe.