A 2023: Goro, Abubak`ar Bichi za su jawo nasarar APC

Goro

Tura wannan Sakon

Daga Alhaji Usman B. Dangwari

Alamu suna kara nunar da cewa, jamiyyar APC mai mulkin kasar nan tana kara yin karfin lashe zabubbukan da ake shirin gudanarwa a shekara ta 2023 idan Ubangiji ya kai mu, musamman yadda wasu daga cikin a jam’iyyar ta tsayar takara kan mukamai daban-dan suke ci gaba da bunkasa jam’iyyar`.

A matsayi na na daya daga cikin ‘yan kasa kuma mai ikon yin sharhi kan al’amuran da ke faruwa, yana da kyau in yaba wa magoya bayan jam’iyyar ta APC, musamman shugabanni da masu ruwa-datsaki, saboda jajircewa da aka yi wajen fitar da ‘yan takara masu nagarta, wadanda suke da goyon bayan al’umma.

Wannan ce ta sanya na ga ya dace in bayyana sahihancin wasu daga cikin ‘yan takarar da aka tsayar, duba da yadda suke kokari da gaske wajen gudanar da wakilcin mazabunsu, tun lokacin da suka fara wakilcin al’ummominsu a majalisun kasa.

Haka kuma, bisa dukkanin alamu, tsarin da jam’iyyar APC ta yi zai taimaka wajen ba ta nasara sosai a zaben 2023, wanda zai kasance cikin yanayi mai kyau da gamsarwa ta kowane bangare na wannan kasa, duk da cewa jam’iyyu da dama sun tsayar da ‘yan takararsu.

A jiharmu ta Kano, na yaba sosai bisa yadda gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dukkanin masu ruwa-datsaki na jam’iyyar suka yi namijin kokari wajen samar da ‘yan takara masu kyau da nagarta domin shiga zabe, domin samar da wakilci mai inganci.

Akwai ‘yan takarar da aka tsayar guda biyu wadanda ko shakka babu nake yi masu kallon riba ga al’umominsu, idan har aka zabe su kan mukamai daban-daban, domin ganin dimokuradiyya tana samar da riba mai amfani ga al’umma kamar yadda aka ga kamun ludayinsu.

A karamar hukumar Bichi, an tsayar da Injiniya Abubakar Kabir Abubakar, wanda aka fi sani da (Abban Matasa) wanda daga shekara ta 2019 zuwa yau ya samar da managarcin ci gaba a mazabarsa, ba tare da nuna banbancin ra’ayi ko bangare ba. Muna matukar alfahari da wannan wakili, wanda kuma zuwan sa ya samar da alheri mai yawa a sassa daban-daban na fadin karamar hukumar Bichi, don haka muna fata cewa al’ummar wannan yanki namu za su sake zabar Injiniya Abubakar Kabir Abubakar, da jam’iyyar APC domin dorawa kan abubuwan da ya faro.

Haka kuma, ina mai amfani da wannan dama wajen bayyana cewa, tsayar da Kwamared Aminu Suleiman Goro a matsayin dan takarar majalisar wakilai ta tarayya daga karamar hukumar Fagge, wanda tun a shekara ta 2011 yake wakiltar wannan yanki. Ya yi abubuwa masu yawan gaske domin kyautata rayuwar al’ummarsa.

A karshe, ina kara jinjina wa mai girma gwamna, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da dukkanin shugabannin jam’iyyar APC, saboda yadda aka hada hannu ake tafiyar da jam’iyyar cikin yanayi mai kyau da gamsarwa. Sannan za mu ci gaba da bayar da goyon bayanmu wajen tabbatar da cewa an gudanar da zabubbukan 2023 lafiya. Alhaji Usman B.Dangwari, Rijiyar Lemo Kuarters, Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *