A Afghanistan:‘Ya’ya mata sun fara zuwa makarantun book

Ya’ya mata sun fara zuwa makarantun book

Ya’ya mata sun fara zuwa makarantun book

Tura wannan Sakon

Rahotanni daga kasar Afghanistan na cewa, ‘yan mata sun koma makarantun sakandare a lardin Arewacin kasar. Sai dai kamar yadda wadansu jami’an Taliban suka bayyana, har yanzu dokar haramta wa ‘yan mata halartar ajujuwa na aiki a sassa da dama na kasar. Sabuwar g

wamnatin mai tsattsauran ra’ayi ta sanar a wani taron gangami da aka gudanar cewa, an kira wadansu mata ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aiki kuma za a biya su albashi, alamun kungiyar na kokarin yi wa al’umma sassauci bayan kwashe kwanaki fiye da hamsin a kan madafun iko.

Bidiyon da kakakin kungiyar Suhail Shaheen ya wallafa, ya nuna ‘yan mata ‘yan makaranta da dama cikin bakaken kaya, wadansu sanye da fararen mayafi wadansu kuma da mayafin fuska, suna zaune kan kujeru suna daga tutar Taliban.

A Kabul, jami’in ma’aikatar ilimi, Mohammad Abid ya ce, babu wani sauyi na siyasa daga gwamnatin rikon kwarya ta Taliban, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, har yanzu ba a bai wa mata ikon halartar manyan makarantu ba.

A watan da ya gabata kakakin kungiyar Taliban, Zabihullah Mujahid ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, ana ci gaba da aiki kan batutuwan ilimi da aikin mata, yana mai cewa, za a bude makarantu, sai dai bai bayyana takamammen lokacin da za a bude ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *