A Arewa maso yamma: APC za ta hada kan ‘ya’yanta

Ministoci masu son yin takara, a ajiye aiki –APC
Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso yamma, ta jaddada aniyar ta na tabbatar da hadin kai a tsakanin mambobinta a daukacin jihohin yankin.

An cim ma matsayar ne a yayin taron jami’an shiyyar Arewa maso yamma na jam’iyyar wanda mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da shiyyar, Salihu Moh’d Lukman ya jagoranta a sakatariyar jam’iyyar ta shiyyar mai lamba 27 Isa Kaita Road Kaduna.

Hakan yana dauke ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na shiyyar APC Arewa maso yamma, Malam Musa Mailafiya wanda aka rarraba ta ga manema labarai.

Mataimakin shugaban na kasa ya bayyana cewa, bisa la’akari da tarihin siyasar Nijeriya yankin Arewa maso yamma yana da mafi rinjayen kuri’u kuma ya lashe zaben wanda ya zama shugaban tarayyar Nijeriya a duk zabubbukan dimokuradiyya da aka gudanar a kasar nan tun daga lokacin.

Ya sake jaddada tsare-tsaren jam’iyyar a shiyyar wajen hada dukkan jiga-jigan da ake da su da rigingimun siyasa suka haifar tare, ta yadda za su ci gaba da rike martabar yankin Arewa maso yamma da aka sani a siyasar Nijeriya.

Lukman ya kara da yin kira ga jami’an jam’iyyar na shiyyar da su jajirce wajen yin aiki tukuru domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara baki daya ta hanyar tabbatar da amincewar da ‘yan jam’iyyar suka yi masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top