A asbitin Malam Aminu Kano: Za a fara shagulgulan makon kula da idanu

- ‘Yan-jarida mata 100 za a duba idanunsu kyauta
Daga Aliyu Umar
A shirye-shiryen da yake yi na fara shagulgulan bikin makon kula da cutar dundumi na wannan shekarar, asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, hukumomin asibitin sun bayyana cewa, ‘yan-jarida mata 100 ne za su amfana da shirin duba lafiyar idanu kyauta,
Makon wanda za a gudanar daga ranar Lahadi 7 ga Maris,2021 zuwa 13 ga Maris,2021, wanda ya kunshi gabatar da jawabai ga jama’a da aiwatar da wadansu aikace-aikacen kiwon lafiya, wanda kwararrun likitoci kan cututtukan da ke addabar idanu za su gudanar da gwaje-gwaje ga marasa lafiyar idanu.
Wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun mataimakiyar daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta asibitin, Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi ta bayyana cewa, a shekara ta 2020, Jami’ar Bayero ita ce ta karbi bakuncin taron makon masu fama da dundumi ko Glaocoma.
A wannan lokacin manyan malamai da masana daga sassan karatu daban-daban na Jami’ar sun gabatar da makalu a kan abin da ya shafi ciwon na dundumi.
Ta kara da cewa, shugaban sashen kula da idanu na asibitin, Dokta Sadiq Hassan, ya shawarci mutane masu shekaru 40 da haihuwa zuwa 50 ko fiye da haka da su rinka zuwa asibiti a-kai-a-kai domin duba lafiyar idanunsu musamman masu fama da Glaucoma.
A karshe,ya yi kira ga kafafen yada labarai da su yayata shagulgulan na masu fama da ciwan na dundumi , daidai da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin kula da masu cutar dundumi.