A Bauchi: Gwamna Bala ya rarraba tallafi ga zakarun musabaka

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya ce, gwamnatinsa za ta dauki nauyin karatun zakarun gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 36 da ya gudana a jihar Bauchi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rufe gasar karatun a dakin taro na sansanin alhazan jihar, inda ya bayar da gudummawar Naira miliyan 10 ga zakarun da kuma miliyan 5 ga alkalan gasar, domin karfafa masu gwiwar hidimatawa littafi mai tsarki.

Bala Muhammad ya ce, gudanar da musabakar a Bauchi babbar dama da alfarma ce ga gwamnatinsa da al’ummar jihar, inda ya yaba wa mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III kan gudummawarsa wajen tabbatar da nasarar ta.

Ya yi amfani da damar wajen kira ga makaranta alkur’ani da su yi amfani da sakonnin da ke kunshe cikinsa tare da gudanar da adduo’in zaman lafiya da walwala da farfadowar tattalin arziki.

Gwamna Bala Muhammad ya yaba wa jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato kan shirya gasar, kana ya yi kira ga malaman addinin Musulunci da su kara azamar fadakar da al’umma da inganta tarbiyarsu domin kaucewa fushin Allah madaukakin Sarki. Da yake yaba wa Amina Idris Muhammad daga jihar Cross River, yarinya mafi kankantar shekaru cikin wadanda suka fafata a gasar.

Bala Muhammad ya ce, shi da uwargidan sa, Hajiya Aisha Bala Muhammad za su dauki dawainiyar karatunta tare da ba ta tallafi na musamman domin inganta rayuwarta, idan Allah ya yarda.

A na sa tsokacin, mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar yaba wa gwamnatin jihar Bauchi kan martaba mahalarta musabakar, kana ya ja hanA Bauchi: Gwamna Bala ya rarraba tallafi ga zakarun musabaka kalin al’umma kan jin kai da tausayawa juna.

Sarkin Musulmi ya kirayi ‘yan Nijeriya musamman ‘yan kasuwa da su kauracewa kara farashin kayan abinci da na masarufi yayin da azumin watan Ramalana ke tunkarowa. Daga karshe, an gudanar da adduo’i na musamman yayin rufe musabakar da al’ummar Musulmi daga lunguna da sakon Nijeriya suka halarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *