A Bauchi: Gwamna ya gwangwaje Dambam, Misau da kayan tallafi

Bala Mohammed
Jamilu Barau daga Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi ya bayar da tallafin jari na miliyoyin nairori sannan ya bude katafaren asibiti da gwamnatinsa ta sabunta.
A ci gaba da zagayawa kananan hukumomin jihar Bauchi domin rarraba ababen dogaro da kai, tawagar gwamnan ta sauka a karamar hukumar Damban, inda gwamnan ya rarraba kayayyakin sana’o’i dabandaban domin al’ummar karamar hukumar musamman masu kananan jari su samu damar dogaro da kawunansu.
Kayayyakin da gwamnan ya rarraba a karkashin shirin”Kaura Economic Empowerment Program” (Keep), sun hada da motocin sufuri da Babura da kekunan dinki da injinan nika da injinan ban ruwa da Naira dubu hamsin-hamsin ga fiye da mutane 500 da kuma sauran kayayyakin sana’o’i dabandaban.
Gwamnan ya yi haka ne da nufin al’umma su samu damar dogaro da kai da kuma bunkasa kasuwanci da farfado da tattalin arzikin jihar Bauchi.
A yayin ziyarar mai cike da tarihi, Kauran Bauchi yana tare da uwar gidansa, Hajiyya Aishatu Bala Muhammed (Sarauniyar Bauchi) da shugabannin jam’iyyar pdp karkashin jagorancin Alhaji Hamza Koshe Akuyam da mataimakin kakakin majalisar dokoki,Danlami Ahmed Kawule, sakataren gwamnatin jiha da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da masu bai wa gwamna shawara da mataimaka na musamman da shugabannin mata da matasa da ‘yan kasuwa da Malaman addinai da masarautan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi da sauran masoya da magoya baya.
Gwamnan ya kaddamar da bude katafaren asibiti (Janaral Hosfital Damban) wanda gwamnatin jihar ta sabunta tare da zuba kayayyakin aiki da ake bukata, wanda shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar pdp, Sanata Walid Jibrin ya jagoranci bude wa.