A Bauchi: Gwamna ya sake yin allurar rigakafi

Gwamnan Bauchi ya sake yin allurar rigakafi
Jamilu Barau Daga Bauchi Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed na jihar Bauchi ya fara kaddamar da kamfen din allurar korona karo na biyu a jihar.
Da yake kaddamar da atisayen a dakin taro na Bankuet Hall, gidan gwamnati, Bauchi, gwamna Bala Muhammed ya gode wa abokan hadin gwiwar ci gaban ma’aikatan kiwon lafiya, shugabannin addini da na gargajiya kan hadin kai, goyon baya da hadin kan da suke bayarwa, wajen yaki da annobar korona a jihar.
“Mun yi matukar farin ciki A Bauchi: Gwamna ya sake yin allurar rigakafi da kasancewa a nan domin shan kwayar rigafin korona karo na biyu kuma bisa la’akari da kididdiga, muna aiki sosai a jihar Bauchi saboda haka ya zama dole mu gode wa masu ruwa da tsaki kan goyon bayan da suke bayarwa domin cim ma nasarar hakan.”
“Dole ne in fada kuma in yaba a madadin shugaba Muhammadu Buhari cewa, a Bauchi, duk lokacin da shugaban kasa ya gabatar da kansa domin wani abu da ni kaina a duk lokacin da na gabatar da wani abu ma mutanen Bauchi sun ba mu goyon baya da girmamamu kuma tare da haka muna matukar godiya.”
Gwamnan ya yi amfani da wannan hanyar ne wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafa wa gwamnatin jihar, dominn tabbatar da wadatar allurar rigakafin, domin tabbatar da yaduwar ‘yan kasar gaba daya. A cikin wata muhimmiyar sanarwa, wakilin hukumar lafiya ta Duniya, Dokta Ahmed Khedr ya ce, gabatar da allurar rigakafinkorona ya taimaka matuka, wajen rage tasirin barkewar annobar a jihar Bauchi ta hanyar rage yaduwar cututtuka da mace-mace.
“Jihar Bauchi ta cim ma gagarumar nasara ta hanyar kai wa har zuwa kashi 84% na mutanen da suka cancanci yin allurar ta 1 ta rigakafin korona. An samu nasarar fitar da kashi na biyu ne ta hanyar tallafi daga kasa da gwamnatin jihar.
A nasa bangaren, shugaban zartarwa na hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, Dokta Rilwanu Muhammed ya jinjina wa gwamna Bala Muhammed bisa goyon bayan da yake bai wa kungiyar korona, domin sauke nauyin da aka dora mata na tunkarar annobar korona a jihar.