A Bauchi: Hukumar lafiya ta jinjina wa shugaban karamar hukumar Misau

Jamilu Barau Daga Bauchi
Hukumar lafiya ta jihar Bauchi ta yaba wa shugaban waramar hukumar Misau Alhaji Abubakar Ahmad (Garkuwan Misau).
Jawabin hakan ya fito daga bakin jami’in kiwon lafiya na karamar hukumar Misau Alhaji Jibrin Ibrahim Muhammed, yayin wata bita na karawa juna sani kan aikin riga kafin cutar shawara watau ‘Yellow Feber’.
Ya ci gaba da cewa yabon ya biyo bayan hadin kai da goyon baya da shugaban yake ba su na yau da kullum domin ganin al’umma suna amfana da magungunan da hukuma suke kokarin bayarwa na lafiya.
A Satin nan dai hukumar lafiya ta kaddamar da riga kafin shawara,
Shugaban karamar hukumar ya tara kansilolinsa da zaurawa da masu unguwanni domin wayar wa jama’a da kai dangane da wannan allura.
Shugaban karamar hukumar Misau Abubakar Ahmad Garkuwan Misau, ya bayyana godiyarsa da wannan karramawa, ya kuma yabawa shi kansa Galadiman magani na karamar hukumar Misau bisa ga kokarinsa ne yasa har shi ma ya samu lambar yabo.
Ya yi kira ga al’umma da su fito domin yin rigakafin shawara ba ta da wata Illa, ya nuna godiyarsa ga al’umma bisa ga yadda suke fitowa lungu da sako domin yin rigakafin.
Daga karshe ya godewa gwamna tare da jagororinsa kamar yadda suke bayar da kulawa ga al’umma musammam ta fannin kiwon lafiya.
Da fatan Allah ya karawa gwamnatin mu albarka, ya ba su ikon sauke nauyin da Allah ya dora masu, Amin.