A Bauchi: Hukumar tsabtar muhalli ta kai ziyarar gani-da-ido

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

Hukumar tsafce muhalli ta jihar bauchi ta kai ziyarar gani da ido wasu sassan yankuna a garin Bauchi.

A zantawarsa da manema labarai ya ce, za su karfafa kwamitin na musamman da wadannan mutane a duk ranar da za a fito shara ya kasance a kwai wakilan jami’n tsaro.

Ya ce, idan an samu matsala da ‘yan sanda to jami’n da yake wakilta kwamishinan ‘yan sanda wanda ya yi ba dai dai ba, to za su mika shi ga wakilin ‘yan sanda.

Jami’n kwamandan na soja yana tare da su za su fita idan abu ya faru sojoji za su mika shi wurin su.

Shi ma a nasa jawabin, kwamishinan tsabtace muhalli na jihar Bauchi, Alhaji Hamisu Mua’zu Shira ya ce, za su fito da wani tsari domin a taimaka a hada kai tare da cewa, a tabbatar da kula da jihar Bauchi da kewaye. domin a tabbatar da tsabta wadda addini ya tabbatar da hakan.

 Kwamishinan ya ce, wannan abin farin ciki ne, kuma wadanda kuma ba su cika ka’idoji wanda suka yi taurin kai basa bin doka suna tabbatar masu ba za su yi kasa a ido ba wajen hadasu da jami’an tsaro. domin tabbatar da cewa, kowa ya bi doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *