A Bauchi manoman rani za su kwashi garabasa -In ji Bappa Misau

Tura wannan Sakon

Daga Sule Aliyu , Bauchi

Alhaji Bappah Aliyu Misau sarkin yamman Misau kuma shi ne shugaban kamfanin samar da takin zamani na jihar Bauchi, ya zanta da manema labarai kan yadda suke kokarin samar da takin ga manoma masu yin noman rani a jihar da kuma jihohin makwabta bayan sun samar da takin noman damina Yaya ake ciki batun taki? Batun taki a daminar bana gwamnatin jihar Bauchi kawai an bata taki tirela 130, wanda dukkan shaguna na kamfanin samar da kayayyakin amfanin gona na jihar Bauchi an samar masu da takin zamani kuma wadattace, bana taki ya wadata kashiga kasaya ka tafine dadinta babu yan Tsakani, saboda an samar da takin a wadace. A daidai lokacin da ake bukatarsa aka samar da shi muna kuma kan ci gaba da yin takin.

Wani irin taki kuke yi? Takin da muke yi shi ne NPK 20- 10-10 shi ne takin da manomammu suke amfani da shi, shi ne kuma ya dace da irin yanayin kasar noma da Allah ya ba mu. Iya takin ne yawanci manoma suka fi amfani da shi ana ureya da saura chemicals guda biyu MOP da DOP akwai kuma wani abu kamar kasa, kasa ce takan hana sinadaran yin takin su narke.

Akwai masu bukata na musamman sukan nemi NPK 15- 15-15 akwai kuma wadanda suke bukatar taki 235-5 duk wadannan taki muna yin su kuma muna da kwararru wadanda suka iya aikin kuma muna da injinan yin taki irin na zamani da muke aikin da su. Ana koko don ribane, ko kuna samun riba? Gaskiya ana samun riba sosai saboda abinda muke yi yafi karfin bukatar jihar Bauchi har jihohin makwabta suna zuwa suna sayan takin Bauchi.

Ka ga jihohin Gombe da jigawa da Yobe sukan zo su sayi taki a gurin mu, kuma sukan yi amfani A Bauchi manoman rani za su kwashi garabasa -In ji Bappa Misau da wadansu daga cikin shagunan sayar da kayayyakin noma dake kusa da su domin su zo su sayi takin a gurin, misali mutanen Damaturu suna zuwa Dambam su saya a shagunanmu , mutanen Gombe sukan Saya a kananan hukumomin Alkaleri da Kirfi, kuma ingancin Takin ya kai ga duk wanda ya gwada sayar da taki domin Bauchi ya san yana samun sakamako mai kyau kwalliya tana biyan kudin sabulu shi yasa muke yin sa bilhakki da gaskiya, saboda ingancinsa kowa ya sayi takin ya san zai sami biyan bukata zai mayar da kudinsa.

Amma akwai korafi da talakawa suke yi na cewa basa ganin takin? Kamar yadda na fada abaya dukkan kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi akwai takin a shagunan kamfanin samar da kayayyakin gona na jihar Bauchi kuma kowa ya kanje ne ya saya mu kai shi kauyuka ne domin sawwakawa talaka. Kuma kowa zai iya zuwa ya saya tun daga buhu daya zuwa buhu 50 ya dauki kayansa akwai shi a wadace.

Idann kuma ka wuce buhu 50 to sai kazo hedkwata kafin ka samu. Amma ana kokawa dacewa Takin yayi tsada? Wannan shi ne ake cewa maganganun ‘yan siyasa, abin da wadansu gwamnonin siyasa suke yi shi ne ba su da kamfanin taki a jihohinsu, amma in lokacin damina ya yi to sai su sayi taki mota tirela 20 sai suce a kaddamar da sayar da taki a kan Naira dubu 6500 idann an ta shi taro ba za ka kara ganin takin ba, jihar Bauchi muna da kamfanin yin takin, kuma shugaban kasa ya ce, kada a sayar wa diloli takin kasa da Naira dubu 8500, su kuma kada su sayarwa talaka ya wuce Naira dubu 9500, saboda ya cire duk wani tallafi da ake bai wa taki, mu kuma a nan Bauchi muna sayarwa gwamnati da takin a kan Naira dubu 8500, ita kuma tana sayarwa a kan naira dubu 8000 kaga ni babu ruwana, kasuwa nake yi kuma dole in yi riba, kaga idan gwamna ya sayi taki a wurina Naira dubu 8500 ya sayar wa talakawansa Naira dubu 8000 shi ya san dalili idan yau Naira dari 500 da yake bayar da tallafi idan ya sayi mota dari biyu ana maganan ya bayar da tallafi na Naira miliyan 60. Amma wadancan masu kaddamar da sayarwa a karamin farashin basa samun sa wanda suka kawo din ma ‘yan bumburutun taki su suke sayewa.

Yaya alakarku da gwamnatocin jihohi makwabta har yanzu suna neman taki a wurinku? Eh wannan shekara ma sun zo jihar Gombe sun turo wani ya zo mun fara magana da su, kan za su sayi takin su yi amfani da shi wajen noman rani, jihar Adamawa ma sun turo wakilansu suna son takin kuma su kama za su kafa kamfanin takinsu na kansu , za mu yi musayar bayanai da su, jihar Filato ma gwamnatinsu sun zo za su sayo takin saboda kamfanin samar da takin da ke samar masu ba zai ya wadatar da su ba, jihohi da dama dake makwabta sun zo za su sayi takin na noman rani tun da yanzu lokacin damina ya wuce. A gaskiya burinmu ya zamana kamfanin taki na Bauchi ya samu karbuwa a dukkan jihohin arewacin kasarnan domin ingancin takin da muke yi kuma za mu fadada kasuwancinmu sosai.

Ganin girman kamfanin ku da dimbin bukatun neman taki da ake da shi a rana kuna samar da taki buhu nawa? A rana idan muka samu babu wata matsala mukan yi mota 10 shi ne buhu dubu 6, watau mukan yi aiki safe ne dana rana. Wadanda suke aiki da safe da yake sukan fara da wuri sukan yi mota 7, su kuwa masu aikin rana suka yi mota biyu zuwa mota uku. Amma wani lokaci in sun kai karfe 9 zuwa 10 na dare mukan yi motoci 11 zuwa 12 a rana.

Kuma kowace mota tana cin buhu 600 ne. saboda sadaukarwa da dogewa na ma’aikatanmu da kuma irin kyautata masu da muke yi.

Wasu irin matsaloli kuke fiskanta? Babbar matsalar da muka samu shi ne lokacin da gwamnatin tarayya ta ce, ta cire hannunta daga tallafi muje mu nemi kudi mu sayi sinadaran yin takin ko kuma mu nemo takardar yarjejeniyar banki, da ake kira bank guarantee, wanna shi ya jawo mana jinkiri na watanni biyu ko uku kafin mu cika sharudansu, sai gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammed Abdulkadir ya tsaya mana muka sami takardar bankin UBA, banda wannan akasin ba wani akasin da muka samu.

Kuma gaskiya tsayawar da ya yi mana ya sawwaka mana abubuwa da yawa wajen gyaran injunan mu a kan lokaci, da kuma biyan albashin ma’aikata ranar 20 ga kowane wata muke biyan albashi, a kamfanin takin babu wanda yake yabin mu bashi ko na minti daya.

Hakan yasa ma’aikatanmu suna cikin annashuwa, muna daukar lebura 200 zuwa 250 suna aiki a nan gidan a karshen sati za su samu Naira dubu 15 ko dubu 20 a wata dubu 60 zuwa dubu 80.

Wata shawara za ka bai wa manoma ganin damina ta kare? Idan an samu amfanin gona kar a gaggauta sayar da shi, domin idann sayar da shi za a samu karancin abinci, domin abincin zai yi tsada, a gaba kuma idan talaka ya samu amfani idan ya samu hali ya sake sayan takin da zai yi amfani da shi a noman rani, ya kuma yi tanadin na shekara mai zuwa, muna kuma shawartar manoma da su nemi ilimin yin amfani da takin zamani domin samun yabanya mai kyau kaga noman da za ka yi shi cikin jahilci idann za ka zuba buhu daya ne sai kaga ka zuba buhu uku kaga asarace ya kama a gwamutsi malaman gona domin samun ingancin ayyukan gona da samun riba mai amfani.

Alhaji Bappah Aliyu Misau Sarkin Yamman Misau, kuma Shugaban Kamfanin samar da takin zamani na Jihar Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *