A Bauchi: Mata, maza sun amfana da tallafin gwamnati kan sana’o’i

Tura wannan Sakon

Sanata Bala ya kaddamar da tallafi na kudade da kayan sana’o’i ga al’ummar yankin kuma ya bayar da kyautar motoci da baburan hawa.

Kasancewar 12 ga watan Yuni na wannan shekara ranace ta tunawa da mazan jiya wanda hakan yasa kasar Nijeriya ta dauki wannan rana da muhimmanci,  a duk shekara kuma a irin wannan rana Nijeriya takan tuna da mazan jiya.

A saman rubutuna na yi bayani cewa, gwamna Sanata Bala cikin adalcinsa da kaunar al’ummarsa yasa ya fito da wani kudiri wanda tunda aka kafa jihar Bauchi babu wani gwamna wanda ya taba irin haka sai shi,  shi dai wannan shi ne na samar wa al’umma abin yi, wanda za su dogara da kansu ba sai su ci gaba da yawace-yawace ba, sannan kuma yin haka zai rage mutane masu zaman kashe wando tun daga maza har mata.

Wannan kudiri da gwamna ya kawo shi tare da gudunmuwar uwargidansa, Hajiya Aishatu Bala Muhammed (Sarauniyar Bauchi ta farko) shi ne su samar wa al’umma abin yi domin dogaro da kansu.

Hakan ya sa gwamna Sanata Bala ya ware zunzurutun kudi, domin al’umma su amfana da wannan kudi a duk fadin wannan jiha ta Bauchi.

Akwai sana’o’i da dama wanda kowa yake so kuma cikin ikon Allah wanda za su ci gajiyar wannan kudi ba wai gwamna ba ne ya kawo su, mutanen garin su ne suka kawo su.

Daga cikinsu akwai wanda za su samu kudi (100,000 da masu 50,000) da masu keken dinki, injin markade, tumaki da awaki, injin gyaran gashi na mata, injin taliya na zamani, da motoci da sauran kayan sana’a.

Sannan kuma shi kudirin da gwamna ya kirkiroshi ba kai ake bayar da wannan abuba akwai takarda da aka riga aka bayar tuni al’umma suka cika, kuma aka ba su horo a kan kasuwanci kafin kowa ya samu tallafi wannan tallafi zai ci gaba da gudana a fadin jihar Bauchi gaba daya.

Kuma haka za’a ci gaba da rarraba wadannan kayayyakin sana’o’i a duk kananan hukuma guda 20 da muke da su a jihar Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *