A Bauchi: Shugabar Basobca ta rarraba kayan karatu

Tura wannan Sakon

Daga Jamilu Barau daga Bauchi

Shugabar hukumar kula da marayu da mararsa galihu na jihar Bauchi (Basobca), Hajiya Yalwa Abubakar Tafawa Balewa ta kaddamar da rabon kayayyakin karatu ga yara marayu da marasa karfi a karamar hukumar Bauchi, a dakin taro na sakatariyan karamar hukumar.

A jawabin shugabar ta ce, kwanakin baya an kaddamar da shirin a fadin jihar baki daya, wanda fiye da yara 7000 ne za su ci gajiyar tallafin kayayyakin karatun.

Ta ce, sun zo ne domin kaddamar da kuma mika Kayayyakin ga shugaban karamar hukumar Bauchi tare da kwamitin rabon kayan.

Hajiya Yalwa ta kara da cewa, dalibai 500 za su ci gajiyar tallafin a karamar hukumar Bauchi, wanda aka zakulo su daga makarantun firamare daban-daban, sannan ta yi kira ga shugaban karamar hukumar Bauchi da ya bayar da gudumawarsa wajen biyan kudin dinkin kayan yaran.

Ta kara da yaba wa gwamna Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi da uwar gidansa, Hajiya Bada Bala Muhammad, bisa goyon baya da suke bai wa hukumar Basobca, tare da nuna kulawa da suke nuna wa akan marayu da mararsa galihu a fadin jihar Bauchi. Daga karshe, ta yi fatan Allah ya saka masu da mafificin alheri.

A jawabin shugaban karamar hukumar Bauchi, Alhaji Mahmood Babamaji wanda ya sami wakilcin mukaddashinsa, Alhaji Salisu Yakubu Uban Doman Zungur, ya ce, sun yaba kwarai da gaske bisa aikin alheri da yake gudunarwa.

Ya ce, babu abin mamaki duba da tarihin gidansu da kuma gudumawar da mahaifinta ya bayar wajen inganta kasar Njeriya, sun kuma ji dadi yadda gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Kaura yake bayar da muhimmacin gaske bisa abin da ya shafi marayu da mararsa halihu Ya kuma bayar da tabbacin cewa, za su bayar da nasu gudumawar a matakin karamar hukuma, domin inganta rayuwar Marayu da mararsa galihu a karamar jukumar Bauchi.

Hajiya Yalwa Abubakar Tafawa Balewa ta sami rakiyan Alhaji Muhammad Zakari Dambam da mataimakinsa Alhaji Ahmad Kawule Aliyu da sauran manya ma’aikatan Basobca ta jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *