A Bauchi: Za a rufe karbar kudin Hajji, 11 ga Mayu –Imam

Imam Abdurrahman Ibrahim

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Bauchi ta yi kira ga maniyyita da suka ajiye Naira miliyan 1 da rabi ko kasa da haka da su cika kudinsu zuwa Naira miliyan 2 da rabi kafin ranar 11 ga watan 5, yayin da ake jiran ayyana kudin aikin hajjin bana daga hukumar Alhazai ta kasa.

Babban bakataren hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya yi kiran a Bauchi yayin da yake jawabi ga jami’an kula da aikin Hajji na kananan hukumomi kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana daga hukumar.

Ya bayyana cewa, jihar Bauchi ta sami takaittun kujeru 1362 na aikin Hajjin bana, inda ya kara da cewa, rabon kujerun zai kasance ne bisa tsarin na farkon zuwa farkon samu.

Dangane da tsadar kudin ajiya Naira miliyan 2 da rabi, Imam Abdurrahman ya danganta yanayin tattalin arzikin a duniya tare da faduwar darajar Naira a kan Dala a matsayin alhakin ayyana kudin ajiyar har zuwa miliyan 2 da rabi.

Daga nan Imam Abdurrahman ya shawarci dukkan wadanda suka yi ajiya a hukumar da su yi amfani da lokaci na musamman wajen biyan sauran kudin, yana mai jaddada cewa, hakan zai bai wa NAHCON hacin kai domin kammala shiryeshiryen aikin Hajjin.

Ya yi amfani da wannan damar domin jaddada aniyar gwamna Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi na samar da yanayi dominn tabbatar da jindadin Alhazan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *