A Billiri: Kamfanin Boska ya duba lafiyar idanu kyauta

Kamfanin Boska ya duba lafiyar idanu kyauta
Danjuma Labiru Bolari, Gombe
A ranar Larabar makon jiya, kamfanin Deda Medica da ke sarrafa maganin nan na Boska ya ware rana ta musamman domin duba lafiyar idanun al’umma kyauta a garin Billiri, jihar Gombe.
Jagororin kamfanin sun ce, sun ware ranar ce musamman domin ilmantar da jama’a muhimmancin lafiyarsu ta hanyar amfani da magungunan kamfanin wajen rage radadin ciwon da ke damun su, a kowacce rana.
Da yake jawabi a wajen taron, a garin na Billiri, kan dalilin ware ranar domin duba lafiyar idanu kyauta, babban sakataren kamfanin, mai kula da yankin Arewacin Nijeriya, Mista Ayodele Opowoye, ya ce, suna so su ji daga abokanan cinikayyarsu yadda suke amfani da magungunansu, su kuma ga ta yadda za su taimaka masu a jihohi bakwai na kasar a cikin watan Yuni, 2022.
Daruruwan ‘yan kasuwa ne da mabukata gami da mazauna garin na Billiri suka dinga tururuwa domin zuwa su ga likitocin da suka zo domin duba lafiyarsu da ta shafi idanu, a ba su tabarau da magunguna kyauta.
A cewarsa, burin kamfanin shi ne ya ci gaba da samar da ingantaccen magani ga abokan cinikayyarsu da kuma daukacin al’umma baki daya.
Wani daga cikin masu amfani da maganin na Boska da ya ci moriyar aikin idon mai suna Joseph Isaac, ya roki kamfanin da ya tabbatar da cewa, shirin ya dore domin taimakon al’umma musamman marasa galihu.
Daga bisani ya gode wa kamfanin bisa kokarinsu na duba lafiyar idanu da bayar da tabarau gami da magunguna kyauta.