A Borno: Kwamandan FRSC ya nuna wa direbobin Tifa yatsa

Labarai Sani Gazas Chinade, Maiduguri
Kwamandan hukumar kiyaye hadura na tarayya, (FRSC) Boyi Utten ya sha alwashin daukar mataki kan direbobin motocin daukar yashi (Tifa) da ke tukin ganganci a babban birnin jihar Borno.
Direbobin da ake samu mafi yawansu matasa ne da ba su dace ba, kuma sun kashe matafiya da dama a tsakanin birnin na Maiduguri da sauran yankuna yayin da suke jigilar yashi daga wannan gefen garin zuwa wancan.
Binciken da muka yi ya nuna cewa a mafi yawan lokuta “direbobin motocin daukar yashin sukan mika motocin ga yaran su da sunan su huta wasu lokutan kuma su yi sallah.
Kuma wadannan yaran da ba su dace ba aksari a matsayin su naa wadanda ba su kware ba a wajen sarrafa wadannan manyan Motoci su ne kan yi ta tukin kan mai uwa da wabi a kan titin Gubio yankin da suke dauko yashi zuwa birnin na Maiduguri.
Da yake amsa tambayoyi kan irin tukin gangancin da wasu daga cikin direbobin tufa (tipper) suke yi a cikin birnin, kwamandan hukumar ta kiyaye hadurra Boyi Utten ya ce, “Eh ina sane da halin rashin tausayin da direbobin masu tuka Tippers suke aiwatar wadda a mafi yawan lokacin ke haifar da salwantar rayuka da dukiyoyi ga wasu masu tsautsayi.”
“Na shirya tattaunawa mai gamsarwa da direbobi da shugabannin kungiyarsu nan ba da jimawa ba kuma za mu fara aiwatar da tsauraran matakai ta hanyar damke masu karya dokar hanya a tsakaninsu.”
“A cewar Sa a kwanakin baya an Sam makamancin hakan yadda jami’an mu suka rika aiwatar da wani aikin ceto wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu su 4 sakamakon danne wasu mutane da wata motar daukar tashin ta yi a birnin na Maiduguri wadda Sam ba mu ji dadin faruwar hakan ko kadan ba don haka dole ne mu dauki matakan kariya don dakile duk wani abin da zai faru nan gaba, don haka fadakarwa ta tattauna da direbobi da shugabannin kungiyarsu.”
Kwamanda Boyi ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da takaici, inda ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin kwararru dake cikin babban birnin na Maiduguri don kula da su.
Akan tukin wuce gona da iri na direbobin tipper a wasu sassan jihar musamman ma hanyar Maidugurin Mafa kwamandan ya ce “Tun da na kama aiki a Borno ban samu labarin wani hatsarin mota da aka yi a kan titin Mafa, Dikwa Gamboru Ngala ba Rundunar FRSC reshen Dikwa dake kula wannan hanyar kuma daga bayanan da nake da ita” ba taba kama wani direban da bai kai shekaru da ya dace da tukin mota ba.
Don haka direbobin wancan bangare tsofaffin direbobi ne wadda hakan ya bambanta da abin da muke da shi a kan titin maiduguri Konduga Bama.
“Ina ganin ba a saba yin hakan ba a kan hanyar Mafa Dikwa kuma saboda kalubalen tsaro wanda ya sa sashin hukumar wanda ya kamata ya kasance a Dikwa yana zaune a maiduguri.
Tippers suna da karancin hadari a wannan hanyar.” In ji Boyi.
Aminiya ta tuna cewa wani direban tipper a baya-bayan nan an yi zargin ya kashe manoma kusan rabin dozin da ke kan hanyarsu ta zuwa gona daga kan titin Baga zuwa mongomeri a kan titin na Baga.
Shaidun gani da ido sun ce “An kashe mata uku ciki har da mace mai juna biyu daga EYN daya daga cikinsu mace ce mai ciki . ”
Cikin wanda wannan hadari ya shafa akwai Wata tsohuwa ‘yar unguwar Dubai da ke kan titin Baga yayin da mata 2 uwa da diya mace ‘yar yankin Chescon daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu ba zato ba tsammani sakamakon rashin kulawar wani matashi da ya rasa yadda zai yi da motar tifa da ya dauko yashi ya afka musu.”