A bukukuwan Sallah: DSS ta yi hasashen samun hare-haren ta’addanci

Tura wannan Sakon

Hukumar ‘Yan-sandan farin kaya ta DSS ta bayyana gano shirin kai hare-hare a kan wuraren ibada da wuraren shakatawa da kuma kadarorin gwamnati, musamman lokacin bukukuwan Sallah.

Mai Magana da yawun Hukumar, Peter Afunanya ya bayyana haka a sanarwar da ya rarraba wa manema labarai, inda yake zargin mutanen cewa, suna shirin mayar da kasar irin halin da ta samu kanta kafin shekarar 2015 inda ake samun fashe-fashen makamai.

Jami’in ya bukaci jama’a da su zuba ido domin lura da abubuwan da suke faruwa a yankunan su, yayin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum, tare da gabatar wa jami’an tsaro da bayanan duk wani abin da ba su gamsu da shi ba a yankunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *