A ceto harshen Hausa daga gurbacewa -Sagir Sani

Daga Ibrahim Muhammad Kano
An yi kira ga masana da iyayen Kasa da masu ruwa-datsaki a jihar Kano kan su dauki mataki domin ceto harshen Hausa daga masu yin kutsen gurbata shi. Mataimakain shugaban Karamar hukumar Dala, Honarabul Sagir Sani ne ya yi kiran a yayin Kaddamar da littafin “Makomarmu” wanda Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta wallafa aka Kaddamar a dakin taro na gidan Mumbayya da ke unguwar Gwammaja a birnin Kano.
Ya ce, ya kamata marubuta Hausa su riKa kare mutuncin harshen, amma abin takaici ne a zo gidajen radiyo da allunan tallace-tallace ana gurbata Hausa.
Mataimakin shugaban Karanar hukumar ta Dala ya Kara da cewa, ya kamata mu nuna ba haka ake yi ba, kuma ba mu yarda ba, mu nuna kishi ga yarenmu na Hausa, wanda yana daga cikin wanda aka fi saurara a Afirika da sauran Kasashen Duniya. Ya yi nuni da cewa, ya kamata duk wani abu da za a yi da harshen Hausa sai an tace shi an tabbatar ya yi daidai da yadda aka sani.
Shi ma a nasa jawabin, tsohon dan majalisar jihar Kano mai wakiltar Kara mar hukumar Birnin Kano, Honarabul Aliko Shu’aibu, wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kano ne, ya nuna takaicinsa a kan gurbacewar tarbiyyar yara, sannan ya ja hankalin ‘yan siyasa a kan su guji jefa yara a hali mara kyau, wanda su kuma ba za ga ’ya’yansu a ciki ba.
Honarabul Shu’aibu ya yi nuni da Kasashe irin su Amurka da na Larabawa da suke kawo tallafi na jin Kai ga al’umma, amma abin takaici a nan mai kudi sai a sami maKocinsa ba shi da abin da zai ci.
A nata bangaren, wacce ta rubuta littafin, Malama Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, wacce jami’ar yada labarai ce a Karamar hukumar Dala, ta ce, da ma ita marubuciya ce kuma abin da ya janyo hankalinta ta rubuta littafin shi ne, duba da irin halin da ake ciki na tabarbarewar tarbiyya a Kasar nan, kuma a matsayinta ta mace uwa, tana ganin yadda matasa suka lalace da rashin tarbiyya.
Ta Kara da cewa, kasancewar tana da Kanne da ’ya’ya, da kuma kishin al’umma da take yi ya sa ta yi nazari ta yi rubutu kan tarbiyya da ilimi, domin ta bayar da gudummuwa wajen kyautata tarbiyyar al’umma.
Hajiya Bilkisu Yusuf Ali ita ce ta gabatar da nazari a kan littafin, tare da yaba wa marubuciyar kan wannan gagarumin KoKari da ta yi da kuma bayyana ‘yan tuntube da aka samu na yawaita amfani da wasu ’yan kalmomi na turanci a littafin.
Shugaban kamfanin Classic One, Alhaji Badamasi Burji ya sayi littafin guda 50 a kan kudi Naira miliyon daya, sai kuma Alhaji Aminu Ladan (Ala) ya sayi guda biyar a kan kudi Naira dubu 500 da sauran mutane da dama da suka bayar da gudummuwa.