A cikin shekaru 10: Fiye da shaguna 80 suka kone a kasuwar Kurmi –Mai Kano

Gobara

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa dake kasuwar Kurmi, Alhaji Abdullahi Maikano ya bayyana cewa, fiye da shaguna 80 ne suka kama da wuta kuma suka kone a kasuwar a lokacin da ta gamu da ibtila`in gobara a shekara 10 da suka gabata.

Shugaban ya ci gaba da cewa, dukiyoyi da kuma kadarorin miliyoyin Nairori aka yi asara. Maikano ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridarAlbishir satin da yawuce.

Ya ce, yanzu haka kasuwar tana bukatar motocin kashe gobara domin dakile gobarar nan gaba. Ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wajen samar motocin kamar yadda aka yi wa kasuwar Kantin Kwari na sama masu motar kwana-kwana.

Daga karshe, Maikano ya yi wa al’ummar Musulmi fatan alheri dangane da wannan watan Ramadan, kuma ya yi kira ga sababbin shugabanni da su ji tsoron Allah wajen gudanar da harkokinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *