A dakatar da rushe kasuwar Bichi -’Yan-kasuwa

A dakatar da rushe kasuwar Bichi
Daga Jabiru Hassan
Yan kasuwar Bichi da ke jihar Kano sun buqaci a dakatar da shirin rushe kasuwar domin sabuntata tare da cewa, shagunan da ke kasuwar suna cikin yanayi mai kyau domin haka suna buqatar a dakatar da maganar rushe kasuwar domin sake mata fasali kamar yadda ake shirin farawa.
Sun nuna bukatar ne ta bakin tsohon shugaban kasuwar, Alhaji Umaru Isa a yayin da Albishir ta ziyarci kasuwar, inda ya sanar da cewa, idan har za a rushe shaguna da rumfunan kasuwar ya kamata a dauki matakai na adalci da sanin ya kamata ta yadda shirin sabunta kasuwar Bichi zai zamo abin alfahari.
Alhaji Umaru Isa ya qara da cewa, kusan dukkanin shagunan da ke cikin kasuwar suna cikin yanayi mai kyau domin haka yana da kyau a dakatar da batun sake fasalin kasuwar musamman ganin cewa, ‘yan kasuwar da yawa za su iya rasa shagunan su sakamakon rushe masu shaguna da za a yi ba tare da daukar matakai masu gamsarwa ba.
Sannan ya nuna yadda ake samun matsaloli duk lokacin da aka rushe kasuwar domin sabunta ta inda wadansu kan rasa shagunan su ko kuma rumfunan da suke gudanar da sana’o in su na cinikayya, sannan ya sanar da cewa, idan har sai an rushe kasuwar domin sake mata fasali to wajibi ne a dubi masu shaguna da rumfuna da ke kasuwar da idon rahama ba tare da wani ya rasa guraren sana’arsa ba.
Alhaji Umaru Isa ya yi amfani da wannan dama inda ya yi kira ga daukacin ‘yan kasuwar da ke da shaguna ko rumfuna a kasuwar da su kwantar da hankalin su tare da ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda domin suna qoqari wajen ganin kowa bai yi asarar dukiyoyinsa ba.
Da yake mayar da martani kan yunkurin sabunta kasuwar, shugaban qaramar hukumar, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo ya shaida wa wakilinmu cewa, ko shakka babu za a yi aikin rushewa da sabunta kasuA dakatar da rushe kasuwar Bichi -’Yan-kasuwa war ba domin a ci zarafi ko mutuncin ‘yan kasuwar ba, illa dai sauya fasalin ta bisa tafiyar zamani bisa la’akari da cewa, qaramar hukumar Bichi ita ce hedikwatar masarautar Bichi.
Sannan ya ce “ Muna masu tabbatar da cewa, babu wanda zai rasa komai nasa kuma ko shaguna nawa mutum yake da su za a ba shi abin sa ba tare da rage koda takun kafa daya ba, haka kuma wannan aiki da za a yi zai kawo ci gaban harkokin kasuwanci da cinikayya da kuma tattalin arziki domin haka muna buqatar hadin kai da goyon baya daga dukkanin ‘yan kasuwa”.
Farfesa Yusuf Muhammad Sabo ya sanar da cewa, tuni aka fara samar da shaguna na wucin gadi domin tsugunar da ‘yan kasuwar kafin kammala aikin sabunta kasuwar, sannan ya yi fatan alheri ga dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar qaramar hukumar Bichi, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ayyuka na majalisar, saboda muhimmin aiki da ya kawo domin ci gaban al’umma.
Mafiya yawan wadanda suka tattauna da wakilinmu sun bayyana cewa, suna son a yi adalci wajen rabon shaguna a kasuwar idan an qammala sabuntata, tare da gode wa tsohon shugaban kasuwar, Alhaji Umaru Isa da mataimakan sa saboda qoqarin da suke yi wajen ganin an yi tsari mai kyau kuma wanda mutane za su gamsu idan an zo rarraba shaguna a kasuwar.