A Dala: Ba mu da dan takarar da ya fi Gawuna inganci –Shatsari

Gawuna, ya cancanci zama gwamna
Tura wannan Sakon

Daga Shafiu A Yahaya

A karamar hukumar Dala ba mu da dan takara da wuce Gawuna. Bayanin haka ya fito daga bakin, Auwalu Al`alawi Shatsari yayin gangami kungiyoyin fiye da 40 da suka yi taro da maidakin dan takarar gwamnan Kano a APC, Hajiya Hafsatu Nasiru Gawuna a karamar hukumar Dala.

Ya kara da cewa, a matsayinsa na makusanci aboki dan uwa ga Gawuna ya san idan kanawa suka zabi Gawuna za su ga ci gaba, kasancewarsa ya yi aiki da gwamnoni uku na Kano hakan ta ba shi gogewa da kuma kishin Kano da ci gabanta a cewar, HonShatsari.

Malan Auwalu Al`alawi Shatsari, shugaban kungiyar Dala Support Organization Nasiru Gawuna watau magoya bayan dan takarar gwamnan Kano Dokta Yusuf Nasiru Gawuna, na APC na karamar hukumar Dala ya ce, bisa dukanin alamu babu wata matsala a zaben gwamnan Kano a karamar hukumar Dala, kuma sun tabatarwa dan takarar gwamnan Kano a APC nasara a wannan yankin dama sauran kananan hukumomi Kano.

A karshe, shugabanin kungiyar Gawuna Enboy, Alkasim Musa Madigawa, daya daga cikin shuganin kungiyoyin da suka shirya gagarumin taron a karamar hukumar Dala ya ce, nagartar Gawuna da dan takar mataimakinsa, Alhaji Murtala Sule Garo, a bayyane yake mutanen Kano sun ga ayyukansu a gwamnatin Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *