A Damaturu: Kwalejin Kimiyya ta tarayya ta dauki dalibai 1,546

Malam Adamu-Adamu
Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
kwalejin kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Garin Damaturu cikin Jihar Yobe ta yi bikin kaddamar da Sababbin Dalibanta na wannan shekakarar karatu ta bana 2019/2020 wadanda za su samu horo kan karatun karamar Diploma da babbar Diploma OND/HND su kimanin 1, 546.
Da yake jawabi yayin kaddamar da sababbin daliban a sabon babban dakin taro na kwalejin Shugaban kwalejin Dr. Usman M. Kallamu ya bayyana cewar, wannan kaddamarwa Na dalibai ne ma su karatun karamar Diploma ND da babbar Diploma HND na shekarar karatu ta 2019/2020 su kimanin1,265 masu karatun ND da kuma 281 da za su yi karatun babbar Diploma a dukkan bangarorin sashi-sashi na kwalejin.
Shugaban kwalejin ya kuma taya sabbin daliban murnar samun wannan dama ta shigowa kwalejin wadda hakan ya ba su nasarar kawo wa ga matsayin rantsar da su bayan da suka yi rijistar shigowa kwalejin.
A cewarsa, “wannan dama da Ku daliban kuka samu na samun sahalewar shugowa wannan kwaleji don gudanar da karatun da zai kai Ku ga cigaba ta bangaren samun takardar karo karatu don amfanuwa ga samun rayuwa mai inganci har ila yau zai kuma sa Ku gyara halayyar Ku ta yadda zaku tafiyar da rayuwar ku dai-dai da bukatuwar al’ummomin ku