A daminar bana: Manoma na cikin garari -Saboda tsadar ladan kwadago

tsadar ladan kwadago

Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Tun farkon faduwar daminar wannan shekara ta 2022, manoma a jihar Yobe ke kokawa kan tsadar kudin kodago da kuma karancin takin zamani da ma hauhawar farashinsa da hakan ya tilasta wa dimbin kananan manoma rage ayyukansu na noma.

A rahoton da wakilinmu ya tattaro na nuna cewa, wannan lamarin ya yi muni, a lokacin da aka fara shuka, yadda farashin kayayyakin aiki da suka hada da motar noma watau Tractors, wadda idan dai mutum yana son ya sami yalwar amfanin gona, ya zama wajibi manomi ya samar da motar noma a gonarsa kafin ya shuka amfanin gona, lura da yadda kasar noman ta ke.

Abin da ya kara dagula lamarin shi ne, tsadar kudin aiki, wanda a shekarar da ta gabata akan biya Naira dubu biyu ga kowane ma’aikaci, inda kwatsam a wannan shekarar farashin ya karu zuwa Naira dubu uku ko ma sama da hakan, ban da ciyarwa a duk rana.

Domin rage tsadar kayayyaki da yin aiki, wasu manoman sun rungumi amfani da taraktoci a matsayin madadin ’ya kodago ta hanyar yin hayar tarakta, domin sauƙaƙe aikin, da sauri da kuma matsakaicin farashi.

Amma abin takaicin a halin da ake ciki, kwatsam sai kudin daukar tarakta ya karu ya zuwa Naira Dubu 150 zuwa sama a rana, wanda ya wuce gona-da-iri.

Bincike ya nuna cewa A daminar bana: Manoma na cikin garari -Saboda tsadar ladan kwadago daukar taraktoci wanda farashinsa ya kai Naira dubu 15 zuwa Naira dubu 20 a sa’a daya kamar yadda yake a shekarar da ta gabata, a halin yanzu ya kai Naira dubu 50 a duk sa’a daya, wanda akan danganta hakan ne da tsadar man dizal, wanda ya tashi daga Naira dari 350 zuwa sama da Naira dari 820 a duk lita daya a halin da ake ciki.

A halin yanzu, manoma na kokawa kan yadda suke noma a kullum da sauran ayyukan da suke yi, saboda illar da ci gaban ya yi wa fannin. Wani Farfesa a fannin Noma a jami’ar Maiduguri, wanda shi ne shugaban tsangayar koyar da aikin na noma na jami’ar jihar Yobe da ke Damaturu, Abba Gambo, ya bayyana lamarin a matsayin babban kalubale ga manoma.

Ya ce, “Abin da ke faruwa a yanzu na aikin share fage ta hanyar amfani da taraktoci ya wuce yadda manoma ke yi. Tarakta tana amfani da man dizal, a shekarar da ta gabata manomi yana daukar hayar tarakta kan Naira dubu bakwai a sa’a daya, amma a bana, tarakta farashin na kaiwa Naira dubu 50 a kowace sa’a.

To, yanzu ka duba yadda manomi zai iya jurewa. Idan kuna magana game da aikin sa’a hudu, hakan yana nufin kuna magana a kan Naira dubu 200, akwai babban kalubale matuka, a bayan haka, har yanzu a cikin tsarin darajar noma, yayin da kuke tafiya, yawancin manoma ba su da damar yin amfani da abin da ake kira nau’in manoma masu bincike da cibiyoyin bincike.” “A da, akwai ingantaccen tsarin tsawaitawa wanda ke daukar bincike daga cibiyoyi da jami’o’i zuwa manoma, amma a halin yanzu, tsarin ya durkushe gaba daya.”

Gambo ya koka kan yadda buhun takin zamani na NPK 15-15-15, wanda a bara ake sayar da shi Naira dubu takwas, amma yanzu ya koma Naira dubu 35.

“Gaskiya wannan farashin yana da wuyar fahimta, saboda manoma ba za su iya ba, yanzu suna neman duk abin da za su yi don ganin an samar da takin a gonakinsu” a cewarsa. “Kamar yadda na fada, karancin abinci yana kara kunno kai, kuma za a fuskanci karuwar laifuffuka daban-daban a fadin kasa matukar gwamnatocin kasar nan ba su samar da kwakkwarar hanyar tallafa wa manoma ba, wajen samun saukin gudanar da ayyukansu na noma ba.”

Babban jami’in kula da gonakin Green Sahara, Suleiman Dikwa, shi kuwa ya yi nadamar cewa, ci gaban zai haifar da raguwar samar da abinci kadan. “Muna da abubuwa da yawa da ke tura farashin kuma babban shi ne farashin makamashi.

“Muna buƙatar duba bayanai masu wuyar gaske, kuma mu yi tambayar cewa, mutane nawa ne za su iya sayen tarakta a tsohon farashi? Mun dade muna rokon a ba mu amsa, ba mu da wata manufa ta noma da kuma inda za mu yi, ba mu da niyya da kuma wani lokacin da za mu iya tantance hanyoyin da ya dace a bi a kan nomanmu”.

Dikwa ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnati ta taimaka wa manoma a wannan lokaci, kuma lamari ne na gaggawa, wanda ke bukatar gwamnatocin su yi hobbasa a kai domin lalubo bakin zaren lamarin, domin amfanin kasa baki daya.

Ya ce, “A wannan lokaci, abin da za mu iya yi shi ne, mu tsara tsarin samun ingantaccen tsari ko duba yadda za mu iya shiga tsakani a matakin farko, wajen kula da sarrafa kayan da sufurinsu da ajiya da mafi ƙarancin farashi a kasuwannin mu.”

“Muna kuma tsara shirin noman rani yadda muke buƙatar yin cikakken gyaran tsarin, musamman wajen rage yawan hukumomi da kuma karkatar da albarkatun zuwa ayyukan ƙara haɓaka aikin na noma, wannan abu ne na gaggawa, wanda ke bukatar tashi daga yadda muke a yanzu ta wajen yin abubuwa a fannin da kuma kasa.”

A karshe ya ce, kamata ya yi gwamnati ta gaggauta mayar da hankali wajen rage asarar da ake samu bayan girbi, domin rage samun cikas, inda ya ce kasar za ta iya ceto sama da dala biliyan 2.4 idan aka dauki matakin cikin lokaci.

Shi ma wani babban manomi, Alhaji Iro Marcha ya ce, kasa za ta iya fadawa cikin yunwa sannu a hankali idan har ba a samar da hanyoyin gaggawa ba domin kamo bakin zaren warware wadannan manyan matsaloli da ke addabar manoma.

Ya kara da cewa, karin farashin makamashi da kayan aiki ya shafi farashin kayan abinci na kiwon kaji da kifi da sauransu a duk fadin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *