A Daura: Buhari ya yi tozali da gwamnoni -Ya fede biri…

Tura wannan Sakon

A ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin APC ya shaida masu abubuwa da dama da suka shafi mulkinsa.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar mai dauke da sa hannu mai taimaka wa shugaban kasa kan yada labari, Malam Garba Shehu ta fitar, ta ce, Buhari ya gana da gwamnonin ne a mahaifarsa ta Daura a gaisuwar Sallah da suka kai masa.

Yawancin kalaman shugaba Buharin dai tuni suka tayar da kura a kasa, inda mutane ke ta yin tsokaci tare da mayar da martani.

Daga cikin abubuwan da shugaban ya fada sun hada da’. ‘Na gaji da mulki’ Shugaba Buhari ya shaida wa gwamonin cewa, ya matukar gajiya da mulkin nan. “Na matsu na tafi. Zan iya gaya muku cewa, abin akwai wahala.

“Sai dai ina gode wa Allah da irin yadda mutane suke yaba mana kan sadaukarwar da muke yi.

‘Aikin yana da yawa’ Shugaban ya bayyana cewa, aikin shugaban kasa yana da yawa. Ya ce, ko a baya-bayan nan yana tausayawa Ministan Harkokin Wajen kasar, Geoffrey Onyema, wanda yake yawan tafiye-tafiye yana barin iyalansa. ‘Na fi gwamnatin baya kokari’ Buhari ya ce, idan aka yi duba kan bayanan da ke kasa, gwamnatinsa ta yi kokri sosai idan aka kwatanta da ta baya. Ya ce, musamman ma a fannin gina abubuwan more rayuwa a kasa.

“Ina yi wa wanda zai gaje ni fatan alheri, a cewarsa. ‘Zan yi kokari a ragowar watannin da suka rage min’ “Badi war haka, zan kammala ragowar wa’adina, kuma zan yi bakin kokarina a ragowar watannin da suka rage min. ‘‘Yan siyasa ku dinga taimako’ Shugaba Buhari ya nemi masu rike da mukaman siyasa da su dinga taimakon ‘yan Nijeriyar da ke neman damarmaki. “Idan kuna da zalama, ba za ku duba ku ga masu bukata ba” a ta bakinsa.

Shugaba Buhari ya shaida wa gwamnonin cewa, ya dade bai je Daura ba kusan shekara daya saboda yawan aiki. Ya ce, Sarkin Daura ne ya ankarar da shi hakan a wajen Sallar Idi. Sai dai ya yi alwashin a can zai ci gaba da rayuwarsa idan ya kammala wa’adin mulkinsa. Shugaban wanda ya saba zama a babban gidansa na Kaduna kafin ya zama shugaban kasa ya ce, garinsa na Daura ya fi masa.

A kan batun tsaro kuwa, Buhari ya ce, yankin Arewa maso yamma na fuskantar kalubale, amma an samu nasarori a yankunan Arewa maso gabas da kudu maso kudancin kasar. Daga nan ya shawarci ‘yan yankin kudu maso kudu da su daina lalata dukiyoyin kasa, wanda hakan ke shafar zamantakewrsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *