A Dawanau: Kungiyar matasa ta shirya gasar kwallon kafa

Kungiyar matasa ta shirya gasar kwallon kafa

Kungiyar matasa ta shirya gasar kwallon kafa

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Lawal Idris

A kusan makonni biyu da suka gabata, kungiyar matasa ta kasuwar sayar da kayayyakin abinci ta Dawanau da ke karamar hukumar Dawakin Tofa suka gudanar da wani wasan kwallon kafa domin lashe gasar cin wani kofi da aka sanya.

Kungiyar ‘yan kasuwar hatsi ta kasa ce ta shirya gasar, a karkashin jagorancin shugaban walwala da jin dadin matasa, Alhaji Abubakar Abdullahi (Dan Habu).

Ya yi godiya ga Ubangiji SWT da ya ba su ikon shirya gasar, domin su karfafa wa matasa gwiwa, musamman wajen fadakar da su kan abin da ya shafi harkokin dogaro da kai, da kuma sanar da su irin illolin shaye-shayen kwayoyi da ke gusar masu da hankali, da kuma tunani.

Abdullahi Dan Habu, ya bayyana cewa, a halin yanzu dole su gode wa Allah, da kuma shugabannin kasuwar ta Dawanau, saboda hadin kan da suke ba su, da goyon baya, wanda hakan ne yasa suke samun nasara a kan duk wasu abubuwa da suka sanya a gaba.

Da yake nasa jawabin, mai magana da yawun kungiyar, Alhaji Mustapha Usman mai-wake, ya bayyana cewa, kimanin kungiyoyi sittin da uku ne (63) suka shiga gasar kwallon kafar, inda kuma a nan ne za a fara da kungiyar ‘yan doya, da ‘yan nika.

A karshe, ya gode matasan saboda samun nasarar da suka yi a wasan, haka kuma ya gode wa masarautar Bichi, da kuma babban jami’in ‘yan sanda da ke kula da kasuwar ta Dawanau, bisa hadin kan da yake ba su, ko da yaushe, a wannan karamr hukuma ta Dawakin Tofa, da ke jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *