A Disamba matatun mai za su fara aiki –Mele

Malam Mele

Malam Mele

Tura wannan Sakon

Labarai daga Aliyu Umar

Shugaban rukunin kamfanonin mai na Nijeriya (NNPC), Malam Mele Kolo, ya bayar da tabbacin cewa, nan da karshen watan Disamba, 2021, za a kammala gyare-gyaren da ake yi, a matatun man Nijeriya.

Malam Mele, ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa, a wajen babban taro na kungiyar editocin Nijeriya (NGE) karo na 17, a dakin taro na rundunar sojojin sama da ke Abuja, a ranar Larabar makon jiya.

Ya ce, cike gibin makamashin Nijeriya shi ne kadai adalcin da ake nema ruwa-a-jallo wajen inganta tsarin tattalin arziki, inda ya dora laifin halin matsin da Nijeriya ke ciki a kan masu-fada-a-ji, kuma ‘yan takarda.

Shugaban ya fito karara ya dora laifin tabarbarewar al’amura kan sace-sacen da barayin gwamnati ke yi, kiri-da-muzu.

Malam Mele, wanda ya kasance bako na musamman a wajen taron, na editocin Nijeriya,

ya kuma ce, tun a shekara ta 1999 gwamnati ke ta hankoran gyaran matatun man Nijeriya guda hudu da ke Fatakwal da Kaduna da kuma guda biyu a Warri, amma abin ya faskara, saboda hujjojin da ya bayar na rashin rikon amana daga wadansu ‘yan-takard

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *