A duniya: Kasashen da suka ci gaba, da noma suke tutiya –Ahud

Daga Musa Diso
Shugaban kamfanin Ahuda Agro & Chemicals Nigeria Ltd, Umar Abdulhamid ya bayyana cewa, babu wata kasa a duniya da za ta ci gaba idan har al’ummarta suka dogara da wata kasa wajen samar da abinci da kuma kayayyakin gona.
Ya ce, sanin kowane cewa, noma shi ne kashin bayan al’umma da kuma ci gaban kasa domin sai da noma kasa take tsayawa da kafarta musamman wajen inganata rayuwar al’umma.
Abdulhamid ya bayyana haka ne ga wakilin jaridar Albishir a birnin Kano satin da ya wuce, ya yaba wa shugaban kasa Muhammad Buhari wajen jajircewarsa na ganin cewa, Nijeriya ta dogara da kanta wajen harkar noma domin Bahaushe ya ce, noma tushen arziki kuma duk wani ci gaba da aka samu a duniya tushen sa za ka ga cewa, daga noma aka samu kuma noma na daya daga cikin sanaa da ke bayar da aikin ga matasa maza da mata domin masana sun ce kashi 90 daga cikin 100 na sana
o`i yana zuwa daga harkar noma. Daga karshe, ya yi kira ga shugabanni masu zuwa da su ci gaba da nuna goyon bayan su wanjen ganin abubuwan da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya fara musamman harkar noma.