A Filato: ‘Yan bindinga sun sace sarkin Gindiri

A Filato: ‘Yan bindinga sun sace sarkin Gindiri

Sarkin garin Gindiri

Tura wannan Sakon

Daga Mohammed Ahmed Baba Jos

An sace Sarkin garin Gindiri na karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato, da misalin karfe 2 na daren Asabar wayewar garin Lahadi, inda mazauna garin suka yi ta jin karar harbe-harbe a fadar sarkin, sannan suka dauke shi, daga bakin wani mazaunin garin mai suna Helen Bulus.

Ta bayyana wa manema labarai cewa, abin ya faru tsakanin karfe 1 zuwa 2 na dare, ta ce ‘yan bindigar sun zo da yawan gaske zuwa fadarsa, a lokacin shi kadai ne a fadar saboda matarsa ta yi tafiya zuwa cikin Jos, hatta ‘ya’yan su su ma ba sa nan, sannan ‘yan bindigar a lokacin suna ta harbi mai tsanani.

A fadar inda mutanen yankin daga wurare dabandaban suka arce, a nasa bangaren mai magana da yawun (operation safe haben) Manjo Ishaku Takwa ya ce, jami’an tsaro da dama suna tabbatar da zaman lafiya a jihar, sannan sun kasance a yankin Gyanbu inda suka yi kawanya domin gano ‘yan bindingar.

Dan majalisa mai wakiltar Mangu ta Kudu Bala Fwagje ya tabbatar da faruwar lamarin, a cewar dan majalisar jami’an tsaro sun bazu a yankunan domin gano masu garkuwar, a nasa bangaren Basaraken Kabilar Mwaghabul watau Miskaham Mwaghabul, shi ma ya tabbatar da kama Basaraken.

Ya kara da cewa, yanzu haka jami’an tsaro suna daji domin ganin sun tseratar da sarkin, shi dai Mista Charles a yanzu haka suna Kotu a kan Shari’ar kujerar tasa ta sarautar fiye da shekaru goma, inda Arch Hudu Manomi ya kai kara kan cewa, an kwace masu sarautar gidan su, inda shi Hudun ya yi nasara a Kotu a bara.

Amma sarkin yanzu ya daukaka kara a Kotun daukaka kara ta birnin Tarayya Abuja, inda tun lokacin tsohon gwamna Jonah Jang ake wannan takaddama, inda ake zargin tsohuwar gwamnatin da kwace sarautar daga gidan su Hudun wanda shi Musulmi ne, kuma shi Kotu ta bai wa nasara a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *