A Gamboru: Zulum, Shettima sun rarraba kayayyakin tallaf

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Daga Maiduguri

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da tsohon gwamnan jihar Sanata Kashim Shettima sun rarraba kayayyakin tallafi hade da kudade ga ‘yan gudun hijirar Gamboru da suka dawo gida su kimanin 60,813 maza da mata don kyautata musu rayuwarsu.

Gwamna Zulum da Kashim Shettima wanda ke wakiltar tsakiyar Borno a majalisar dattawa ta kasa da suka yi tattaki har zuwa Gamborun ta hanyar mota daga Maiduguri a ranar farko sun bayar da kayayyakin tallafin da suka kunshi kayan abinci da kayayyakin amfanin yau da kullum ga mutane kimanin 55,253 daga Gamboru da Ngala.

Cikin mutanen da suka amfana da wadannan kayayyaki sun hada da mata 39,903 wacce kowaccen su ta samu Naira dubu 5 yayin da kowaccen su aka ba ta zanin daurawa, su kuma magidanta su kimanin 15,350 kowannen su aka ba shi buhunan shinkafa mai nauyin kilogram 25 hade da buhunan masara mai nauyin kilogram 25 ga kowannen su.

A rana ta biyu a ziyarar ta su sun kuma rarraba makamantan wadannan kayayyakin tallafi ga ‘yan hijirar da ke garin Wulgo kimanin mutane dubu 5,560 duka dai cikin karamar hukumar Ngala. Cikin ‘yan gudin hijirar, dubu 3,360 mata ne wadanda kowaccen su aka ba ta Naira dubu da turamen zannuwa ya yin da kimanin maza dubu 2,200 kowannen su ya samu buhunan shinkafa da masara ma su nauyin kilogram 25.

Gwamna Zulum da Sanata Shettima yayin ziyarar ta su sun samu rufa bayan wadansu ‘yan majalisar wakilai ta kasa da ke wakiltar kananan hukumomin Ngala da Bama da Kala-Balge sai kuma wasu kwamishinonin da suka hada da Dokta Zainab Gimba da Injiniya Mustapha Gubio na ma’aikatar aikin gona, sai Injiniya Bukar Talba na ma’aikatar kula da kawar da talauci da Nuhu Clark da ma’aikatan ma’aikatar kula da harkokin al’umma da sauran masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *