A gangamin siyasa: Alpha Dambatta ta jinjina wa Farfesa Hafsat Ganduje

A gangamin siyasa: Alpha Dambatta ta jinjina wa Farfesa Hafsat Ganduje

Tura wannan Sakon

Jabiru A Hassan,

Daga Kano An yi bikin qaddamar da qungiyar yaqin neman zaven jam’iyyar APC, wadda Hajiya Alpha Dambatta ta kafa domin ganin jam’iyyar ta lashe zave a shekara ta 2023 tun daga sama har qasa. Qungiyar, wadda za ta yi aiki domin nasarar xan takarar shugabancin qasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, da xan takarar gwamnan jihar Kano, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, da sanatan Kano ta arewa, Barau Jibrin Maliya da na majalisar tarayya, Injiniya Hamisu Chidari, da kuma na jiha, Thomas.

A jawabinta na maraba, Hajiya Alpha Dambatta ta ce, ta kafa qungiyar ne domin qara haxa kan matan qananan hukumomin Xambatta da Makoda wajen tafiya da murya xaya, domin ci gaba da samun ribar dimokuraxiyya a qasa baki xaya. Ta ce, wajibi ne matan jihar Kano su saka wa maixakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abullahi Umar Ganduje, bisa ganin an cim ma nasarar zavuvvukan shekara ta 2023, inda ta qara da cewa, maixakin gwamnan jihar Kano ta yi qoqari wajen kyautata rayuwar mata kamar yadda ake gani a halin yanzu. Hajiya Alpha Dambatta ta sanar da cewa, matan jihar Kano ba za su manta da Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ba saboda jajircewar da take yi wajen tabbatar da cewa matan jihar da yara qanana suna cikin yanayi mai kyau.

Ta kuma yaba wa gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, bisa yadda gwamnatinsa ta sanya mata cikin sha’anin gudanar da gwamnati a fadin jihar, wanda hakan ne ya sanya ta kafa wannan qungiyar domin yin yaqin neman zave ta yadda jam’iyyar APC za ta lashe babban zaven da za a gudanar nan gaba kaxan. A qarshe, Hajiya Alpha Dambatta ta yaba wa matan qananan hukumomin Dambatta da Makoda, bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyya ta APC tun da aka kafa ta, tare da jaddada cewa, wannan gwagwarmaya za ta zamo masu alheri a dukkanin matakai na gudanar da jagoranci. Da take nata jawabin, babbar baquwa kuma wakiliyar maixakin gwamna, wadda ita ce ma’ajin jam’iyyar APC ta jihar Kano, Hajiya ’Yar Dada Maikano Bichi, ta sanar da cewa, Hajiya Alpha Dambatta ta cancanci yabo da fatan alheri saboda yadda take riqe da amanar maixakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abullahi Umar Ganduje tun lokacin da aka kafa jam’iyyar ta APC.

Ta shaida wa Hajiya Alpha Dambatta cewa, “maixakin gwamnan, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje tana jinjina maki saboda qoqarin da kike yi wajen rike amanar tafiyar da ake yi da kuma yadda kike qoqari wajen bunqasa jam’iyyar APC a qananan hukumomin Dambatta da Makoxa”, Ta kuma gode wa matan qananan hukumomin Dambatta da Makoxa, saboda qaunar da suke yi wa jam’iyyar APC da gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje. Taron ya nunar da cewa, jam’iyyar APC tana da cikakken goyon bayan matan qananan hukumomin Dambatta da Makoxa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *