A ganina: APC, a bai wa Kwankwaso mataimakin shugaban kasa

Sanata Kwankwaso

Tura wannan Sakon

Daga Alhaji Usman B. Dan Gwari

A matsayina na dan kasa kuma mai ikon yin magana kan al’amuran da suka shafi kasarmu, ina mai amfani da wannan dama domin bayar da shawara ga mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyyarmu ta APC da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma dukkanin masu ruwa-datsaki a jam’iyyar APC da su bai wa tsohon gwamnan jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso takarar mataimakin shugaban kasa, domin ci gaban kasarmu.

Duk da cewa muna da bambancin jam’iyya, amma dai bai wa Kwankwaso takarar mataimakin shugaban kasa zai haifar da alheri wajen bunkasa wannan kasa tamu mai albarka, musamman ganin cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso yana da kyawawan manufofi ga wannan kasa tamu, kuma shi ne ya dace ya kasance mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Bugu da kari, ina mai jaddada cewa, Kwankwaso jagora ne mai kaifin basirar mulki da samar da ci gaban al’umma ba tare da nuna bambancin ra’ayi ko na kabila ba, wanda hakan ake bukata ga shugaba a tsari irin na dimokuradiyyar wannan zamani, tare da fatan cewa, za a duba wannan shawara tawa domin samar da managarcin ci gaba a kasar nan.

A karshe, nan gaba kadan zan bayyana dalilai guda 7 da suka sanya nake bayar da shawara dangane da daukar Kwankwaso a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, duk da cewa ba ma cikin jam’iyya daya da shi, illa bukatar ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *