A Gombe: Apc ta Gwangwaje ‘Ya’yanta da Babura 15

Tura wannan Sakon

Daga Danjuma Labaru  Bolari, Gombe

A lokacin da zaven shekarar 2023 ke ta qara qaratowa jam’iyyun siyasa ke ta qoqarin ganin sun riqe ‘ya’yansu ba tare da sun bar su ba, jam’iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta rarraba wa waxansu matasa 15 babura qirar Haujoe da Jinchen Kasea.

Da yake jawabi a wajen bayar da baburan, shugaban jam’iyyar APC na jihar Gombe, Mista Nite K Amangal, ya ce, waxannan babura waxansu na kusa da gwamna ne da suka ci gajiyar siyasa suka bayar a rarraba wa matasan da suka yi wa jam’iyya wahala.

Amangal, ya samu wakilcin sakatarensa Sadiq S Goro, ya ce, irin tallafin ga matasa yanzu aka fara domin nan gaba kaxan za a sake ayyuka a kuma bai wa waxansu ba kuma babura kaxai za a rarraba ba, har da motoci da mukama siyasa.

 Ya ce, idan ‘yan siyasa suka yi na su sannan shi A Gombe: apc ta gwangwaje ‘ya’yanta da babura 15 ma gwamna ya yi kowa zai samu domin shi kan nasa babban ne saboda zai xauki mutane aikin gwamnati waxansu za a ba su muqaman siyasa waxansu kuma motoci waxansu babura da sauransu.

Shi ma shugaban matasa Kawu Top Lero, ya bai wa waxanda suka bayar da baburan ya yi inda ya ce, sun yi rawar gani ba su so kansu ba domin daga cikin irin alherin siyasa da suka samu ne suka cire wani abu aka sayi baburan aka rarraba wa matasan kuma waxansu ma na hanya.

Kawu Lero, ya jawo hankalin matasan da cewa, kar waxansu ‘yan adawa su rinjaye su a kan waxansu ‘yan kuxi kaxan ko a yi masu alqawari su bar jam’iyyar APC su koma wata jam’iyya da ba ta san amfaninsu ba.

 Shi ma Sakataren tsaretsare na jam’iyyar, Sunusi Abdullahi Ataka, sake kiran matasan ya yi da cewa, su zama masu aiki da hankali kar waxansu su cusa masu ra’ayi a masu alaawarin da ba za a iya cika masu ba su bar abin da suke gani na zahiri su kama gaibu.

Sunusi Ataka, ya yi amfani da damar wajen yin kira ga ‘ya’yan jam’iyyarsu ta APC musamman masu riqe da muqaman siyasa da cewa, duk abin da za su yi su dinga shigar da jam’iyyar ciki saboda mutunta jam’iyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *