A Gombe: PDP ba ta bukatar yakin neman zabe -Hajiya Uwani Hamsal

Tura wannan Sakon

Daga Danjuma Labiru Bolari, Gombe

Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta ce, ba ta bukatar yin yakin neman zabe a jihar Gombe da ma kasa baki daya, saboda a lokacin da take mulki a jihar kowa ya gani a kasa, ba kamar a yanzu lokacin mulkin APC ba.

Hajiya Uwani Usman, wadda aka fi sani da Uwani Hamsal ce ta bayyana haka a Gombe, a lokacin da take bayyana yadda jama’a suka  gaji da mulkin kama-karya da jam’iyyar APC take yi na rashin kyautata wa al’umma.

Hajiya Uwani Hamsal, ta kara da cewa, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Muhammad Jibrin Dan Barde, shi ne dan takarar da jam’iyyar PDP ta tsayar, kuma shi ne zai cire wa al’ummar jihar kitse a wuta.

Hamsal, wadda ita ce shugabar mata ta karamar hukumar Gombe, kuma shugabar kungiyar Reporters Awareness a gidan Dan Barde, ta ci gaba da cewa, ko yanzu aka fito zabe, PDP a shirye take, kuma in Allah ya yarda ita ce ke da nasara.

A cewarta, idan lokacin yakin neman zabe ya yi, jam’iyyarsu ba sai ta yi kamfen ba, saboda tuni APC ta yi musu, inda ta bayyana cewa, idan suka tashi kawai dorawa za su yi daga inda APC ta tsaya, ma’ana, ta yi musu, bisa yadda ta watsa wa al’umma kasa a ido, an kuma gaji da su.

Hajiya Uwani, ta ce, gwamnatin APC ta shekara uku a karagar mulki, amma ba su da wani abu da za su nuna wa mutane da za su yi kamfen da shi, sai yunwa da fatara.

“Dan Barde, shugaba ne abin misali, wanda idan ya ci zabe kowa zai shaida, domin a yanzu ma da ba shi ne gwamna ba, yana yin iya kokarinsa wajen yin adalci” inji ta.

Ta kara da cewa, Dan Barde ya yi alkawarin zai tallafa wa mata idan ya ci zabe, domin su ne rabin al’umma, sannan a manufofinsa zai inganta bangaren ilimi da tsaro da walwalar al’umma.

Daga karshe ta bayyana cewa, yadda mutane ke ta fita daga APC shi ne yake kara ba su kwarin gwiwa, kuma zaben jihar Osun ya zama zakaran gwajin dafi na cin dukkanin zabukan da ke tafe a 2023, lokacin da Dan Barde zai kayar da dan takarar APC, ya dauki kujerar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *