A Ikko: Hukumar hana fasa-kwabri ta kama jirage da kayan sojoji

Hukumar hana fasa-kwabri, shiyar jihar Ikko, ta ce, ta kama jirage marasa matuka da kayan sojoji da wadansu miyagu suka yi fasa kwabrin su.
Hukumar da ke kula da filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Ikko ta bayyana haka ne ranar Talatar da ta gabata kuma ta kiyasta cewa, kudaden kayayyakin da aka yi fasa kwabrin su sun tasam ma Naira miliyan 300.
Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da ‘yan bindiga suka tarwatsa layin dogo da ya sada Abuja da Kaduna inda suka kashe tare da sace fasinjojin jirgin wadanda ba a ambaci sunansu ba.
Hukumar hana fasa-kwabrin ta ce, za ta mika kayayyakin da ta kama ga sojoji da sauran hukumomin gwamnati da suka dace domin zurfafa bincike kan lamarin.
Wannan ba shi ne karon farko ba da ake safarar haramtattun kayayyaki cikin Nijeriya da suka hada da muggan kwayoyi da makamai da sauran kayayyakin da aka kaucewa biya masu harajin fito.