A Ikko: Shugaba Buhari ya bude kamfanin taki – Mallakin Dangote

Tura wannan Sakon

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci qaddamar da kamfanin samar da takin zamani da ke cikin katafariyar matatar man fetur mallakin Aliko Dangote a jihar Ikko.

Matatar da ke matsayin irinta ta farko kuma mafi girma a nahiyar Afrika, wadda aka kashe tsabar kudi dala biliyan 2 da rabi, da kuma ake sa ran ta samar da taki tan miliyan 3 duk shekara.

Baya ga sashen samar da takin zamanin, sashen matatar man fetur da ake sa ran ya fara aiki shi ma dai cikin shekarar nan za ta rinqa samar da ganga dubu 650 kowacce rana.

Shugaban Muhammadu Buhari ya yaba da tsarin samar da takin da shakka babu zai taimaka wajen samar da guraban ayyukan yi a qasar da sake farfado da tattalin arzikin Nijeriya.

A bikin da ya gudana a Ikko, an samu halartar gwamnoni da sarakunan gargajiya da wakilan jama’a. Shugaba Buhari ya jaddada goyon bayansa ga ayyukan samar da takin daga cikin gida zuwa qasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *