A Ingila: Guardiola ya zama gwarzon manajan shekara

Tura wannan Sakon

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya lashe kyautar gwarzon manaja na wannan kaka, kyautar da hadakar kungiyar manajoji ke bayarwa a duk shekara

. Wannan ne karo na 3 da Guardiola mai shekaru 52 ke lashe kyautar ta Sir Aled Ferguson wadda manajoji daga dukkanin sassa ke kada kuri’a don fitar da gwanin shekara.

Dama dai Guardiola dan Spain tun ya lashe kyautar zakaran manajojin Firimiya bayan lashe kofin gasar karo na 3 a jere kuma na 5 cikin shekaru 6.

Guardiola ya zama manaja na 3 da ya taba lashe kyautar ta gwarzon manajan shekara sau 3 ko fiye, wanda ya bashi damar zuwa dai dai da Dabid Moyes ko da ya ke har yanzu Sir Aled Ferguson na gabanshi da kyautukan 2, wanda a lokacinsa ya lashe kyautar sau 5.

A bangare guda mai horar da kungiyar kwallon kafar mata ta Chelsea Emma Hayes ta lashe gwarzuwar manajar mata, wanda ke matsayin karo na 4 da ta lashe kyautar a jere kuma karo na 6 a jumulla.

Gwarzuwar manajar ta Chelsea dai Emma Hayes ta lashe kofin lig din mata da kuma kofin FA karo na 3 a jere bayan doke Manchester United a wasan karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *