A Jama’are: Ambaliya ta zama barazana a unguwar Sabon Layi

Ambaliya: Zangon Kabo ya jajanta wa ‘yan-kasuwar Kwari

Ambaliya a kabo

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

Al’ummar unguwar sabon layi da ke karamar hukumar Jama’are a jihar Bauchi sun gamu da Ibtila’i na ambaliyar ruwan sama, inda ruwan yai barna mai yawa har wadansu suka rasa matsugunansu.

Ambaliyar ruwan ya jawo gidaje da yawa a fadin unguwar sun rasa matsugunansu, dabbobinsu, kayayyakinsu da abincinsu wanda ya hada da shinkafa, wake, gero, masara da dai saura kayan amfani, duba da haka muna kira ga wanda lamarin ya rataya a wuyansu da su agazawa wanda ibtila’in ya afku masu domin rage masu radadin halin da suke ciki. Al’ummar yankunan sun ce ba su taba shiga cikin mawuyacin hali na ambaliyar ruwan sama ba kamar na wannan lokacin.

Muna rokon wadanda lamarin ya rataya a wuyan su da su duba girman Allah su shigo lamarin domin fitar da mutanen wannan yanki daga halin da suke ciki. Ina jajantawa wa ‘yanda ibitila’in ya afuku masu.

Da fatan Gwamnati za ta duba domin ganin an ceto al’umma daga cikin wannan musiba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *