A jawo hankulan iyaye kan zaben 2023 -Hajiya Kubra Ibrahim

Hajiya Kubra Ibrahim
Daga Alhussain Kano
Ganin yadda zaben 2023 ke kara kusantowa shugaban riko na jam’iyyar matan Arewa da ke jihar Kano, Hajiya Kubra Ibrahim Dankani, ta jawo hankulan iyayen yara musamman mata da su lura tare da sanya idanu a kan tarbiyar yaransu.
Hajiya Kubra, ta ce, sa idon da za su yi shi ne ka da su yarda wadansu su yi amfani da yaransu wajen tayar da hankula a lokacin yakin neman zabe da kuma bayan sanar da sakamakon zabe.
Shugabar rikon na jam’iyyar matan Arewan bayan wannan iyayen yaran su rinka sannin su wa yaran suke hulda da su su kuma su tabbatar ba sa mu’amala da yaran da suke amfani da miyagun kwayoyi.
Kubra Ibrahim Dankani, ta nuna damuwar ta a kan yadda wadansu ‘yan siyasar kasar nan suke bai wa matasa miyagun kwayoyi ko kuma yawo da manyan makamai wanda hakan ke matukar barazana ga rayuwar matasan kasar nan ya kamata su ji tsoron Allah su daina su sani ranar gobe kiyama Allah zai tambaye su ranar gobe kiyama.
Hajiya Kubra ta ce, za ta yi amfani da shugabancin ta na riko wajen wayar da kan matan jihar muhimmancin jam’iyyar, kuma har ila yau kofa a bude take ga dukkan macen da take son shigowa cikin jam’iyyar, sannan ranar zabe su tabbatar sun zabi shugabanni masu tsoron Allah da kuma rikon amana kamar yadda tsohuwar shugabar jam’iyyar, Hajiya Ummi Tanko Yakasai ta yi a lokacin shugabancin ta gaskiya shugabancin ta abin farin ciki ne Daga karshe, ta yi addu’ar Allah ya bai wa jihar Kano da kasa baki daya zaman lafiya da kwanciyar hankali ta kuma yi addu’ar Allah ya sa a gudanar da zabe lafiya ya ba mu shugabanni nagari masu tsoron Allah da sun ci gaban al’umma.