A Jigawa: AFAN ta kai wa Dan-modi ziyarar nuna goyon baya

Tura wannan Sakon

Jabiru Hassan, Daga Dutse

Kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Jigawa watau (AFAN) ta kai ziyara ga dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC, Malam Umar Namadi Dan Modi domin jaddada goyon bayanta ga takararsa a babban zaben da za a gudanar na 2023.

Kungiyar AFAN ta jaddada cewa, ta goyi bayan takarar domin ganin an ci gaba da bunkasa sana’ar noma duba da yadda gwamnatin Muhammad Badaru Abubakar ta duki fannin noma da muhimmancin gaske wanda kuma hakan ta sanya aka sami ci gaba ta fuskar wadata kasai da abinci a fadin jihar.

Da yake yi wa wakilin mu karin bayani kan wan nan ziyara da suka kai wa Malam Umar Namadi, shugaban kungiyar AFAN, Alhaji Idris Yau Mai Unguwa ya ce “mun kai wa dan takarar gwamna ziyara saboda goyon bayan mu na a ci gaba da bunkasa noma a jihar Jigawa kamar yadda gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya yi mama”.

Mai Unguwa ya kara da cewa, bisa la’akari da kwarewa irin ta Malam Umar Namadi, manoman jihar Jigawa za su ci gaba da amfanar dukkanin wadansu tsare-tsare da suka shafi noma a jihar musamman ganin cewa, wanda aka tsayar yana takarar gwamna shi ne mataimakin gwamna wanda kuma ya san matsalolin manoma.

Daga karshe, Idris Yau Mai Unguwa ya sanar da cewa, kungiyar AFAN za ta yi aiki sosai domin ganin an sami nasarar zabe ta yadda sana’ar noma za ta kara samun kula wa daga gwamnatin jihar Jigawa ba tare da an sami tsaiko ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *