A Jigawa: Ana biyan ‘yan-fansho a kan kari -Kwamared Kanya

Tura wannan Sakon


Masu karbar fansho maza da mata da ke jihar Jigawa suna karbar kudadensu a kan lokaci da zarar lokacin ya yi babu bata lokaci.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ma’aikata ta jihar, Kwamared Sunusi Abdu Kanya, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Kwamared Sunusi Abdu Kanya, ya ce, duk ma’aikacin da ya yi ritaya, gwamnatin jiha tana ba shi hakkin sa a kan lokaci saboda haka jihar tana da tsari mai kyau a kan garatuti da kuma fansho, wannan ya sa shugaban kungiyar wadansu jihohin suke koyi da su.

Ya kuma nuna farin cikinsa a kan yadda kungiyar a jihar Jigawa take kara samun ci gaba da kuma zaman lafiya tsakanin kungiyar da gwamnatin jihar da kuma kungiyar Kwadago.

Sannan wani abu da kungiyar take yi shi ne, idan dan kungiya ya mutu ukan yi bakin kokari wajen tallafa wa iyalan sa sannan idan watan Ramadan ya kama sukan rarraba kayan masarufi kyau ta ga ‘yan kungiyar.

Daga karshe, ya nuna farin cikinsa da kungiyar ta jihar Kano ta karramashi, wannan shi zai kara masa kwazo wajen ci gaba da gudanar da aikin kungiyar da yardar Allah.

Shi ma ana shi jawabin shugaban kungiyar na jihar Katsina, Kwamared Zailani Isyaku Kofar Bai, ya ce, kungiyar a jihar tana samun ci gaba kamar yadda sauran jihohi suke samu.

Sannan tana da kyakkyawan fahimta tsakaninta da gwamnatin jihar Katsina, ya yi kira ga gwamnatin jihar dama na sauran jihohin kasar nan da su rinka cike guraben ma’aikatan da suka yi ritaya. Shugaban TUC na jihar Kano, Kwamared Mansur Isa Adamu, a na sa jawabin ya nuna farin cikinsa da kungiyar ma’aikatan ta jihar Kano. Ya ce, kungiyar a jihar tana samun ci gaba sai ya yi kira a gare su da su ci gaba da hadin kan. Daga karshe, ya gode wa kungiyar da suka karrama shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *