A jihar Bauchi: Mai garkuwa da mutane ya fada tarkon jami’an tsaro

A jihar Bauchi: Mai garkuwa da mutane ya fada tarkon jami’an tsaro
Jamilu Barau daga Bauchi
Kwamishinan ‘yansanda a jiha Bauchi, Sylbester Abiodun Alabi ya bayyana hakan wa manema labari a Bauchi yayin da ya gabatar da gungun masu aikata laifuffuka a sassan jihar dabam-dabam.
Ya kuma bayyana cewa, sakamakon rahoton jami’an ‘yan-sanda na farin kaya sun cafke Sunusi lauwali Alais na kauyen Gudale a karamar hukumar Ningi sai ya bayyana wa jami’an ‘yan sandan cewa, ya gudo ne daga kauyen Tunga a jihar Filato yadda a cewarsa, yake tono Kuza har na tsawon shekaru biyu kafin ya koma kauyen Gudale da ke Ningi, sannan ya ambaci wani mai suna Ali da Bammi welcome a matsayin abokan aikata ta’asarsa.
Rundunar ‘yan-sandan ta yi alwashin zakulo sauran bata-garin a duk indasuke. Haka kuma ta yi nasarar kama Ibrahim Adamu dan shekaru 27 da wani mai suna Musa wanda aka fi sani da Nature dan shekaru 45 da zargin yin garkuwa da kashe Alhaji Abdullahi Abdullahi da ke da zama a garin Magama gari a karamar hukumar Toro tare da matansa biyu suka karbi kimani Naira million daya da dubu dari biyu.
Rundunar tsaron ‘yan-sanda tayi nasrar cafke wani mai garguwa da mutane bayan ya tsere daga jihar Filato domin neman mafaka a jihar Bauchi. Kwamishinan ya bayyana hakan ga manema labari a Bauchi yayin da ya gabatar da gungun masu aikata laifuffuka a sassan jihar.