A jihar Bauchi: Mata 3000 sun amfana da tallafin uwar gidan gwamna

Tura wannan Sakon

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya Kara jaddada aniyarsa na yin aiki tuKuru domin ganin dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da dukkan ‘yan takara a KarKashin PDP sun samu nasara a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da uwargidan gwamnan jihar, Hajiya A’isha Bala Muhammed ta Kaddamar da rabon tallafi ga mata dubu 3 a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda ya shaida wa taron cewa, Bauchi za ta bai wa Atiku Abubakar Kuri’u masu tarin yawa domin tabbatar da samun nasara a Nijeriya.

Uwar gidan dan takarar shugaban Nijeriya a PDP, Hajiya Titi Abubakar ce ta kasance babbar baKuwa a yayin taron. A nata jawabin, Hajiya Titi Atiku Abubakar, ta yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su tallata tare kuma da bayar da Kuri’unsu dana ‘yan uwansu ga jam’iyyar PDP domin samun ribar dimukuradiyya.

Tun da farko, Uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Aisha Bala Muhammed ta nuna godiya ga gwamna Bala bisa yadda ya Karfafa mata gwiwa wajen tallafa wa mata domin dogaro da kai.

Ta kuma yi godiya na musamman ga Hajiya Titi Abubakar uwar gidan dan takarar shugaban Nijeriya a PDP da ta amsa gayyatarta ta halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *