A jihar Kaduna: Zaben kananan hukumomi ya bar baya da kura

Kaduna ta ciyo bashi har wuya -PDP
Tura wannan Sakon

A jihar Kaduna har yanzu ana ci gaba da ta da jijiyoyin wuya kan zaben kananan hukumomin da aka yi a farkon watan Satumban 2021.

Lamarin na faruwa nebayan matakin da hukumar zaben jihar ta dauka na ayyana cewa zaben kananan hukumomi guda hudu a cikin 19 bai kammala ba.

A bangare guda kuma, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke ikirarin cewa ita ce ta lashe akasarin kujerun kananan hukumomin da ta ce ana kokarin hana ta, jam’iyyar APC mai mulki a nata bangare na cewa lamarin ba haka ba ne.

Jam’iyyar PDP ta zargi hukumar zabe da zama ‘yar amshin shatar bangaren gwamnati, na yanke shawarar jingine zaben kananan hukumomi biyu da suka hada da Jama’a, da Kaciya, da Jaba da kuma karamar hukumar Siba, saboda rashin kammaluwar zaben da ta ce kotu ce kadai za ta yanke hukunci.

Sakataren jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Aliyu Solo ya ce, hukumar zabe ta koma bangaren gwamnati. “Abin da aka yi a karamar hukumar Giwa da Igabi da Zariya shi ne duk inda aka san PDP za ta yi nasara ba a kai akwatin zabe ba, domin haka za mu kai kara gaban kotu domin a dawo a sake yin zaben a wadannan kananan hukumomi.”

To sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta bakin Muhammad Lawal Shehu Molash, mataimaki na musamman kan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Kaduna, ya yi watsi da zargin inda ya ce rashin kunya ce ta sanya PDP ke wannan magana.

“A adalci irin na gwamnatin Malam Nasiru ElRufa’i, har sun samu sun ci kujerun ciyamomi, wanda idan a lokacinsu ne ba za a taba samun hakan ba, sun ce za su je kotu mu na jira mu ma sai mu je kotun.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *