A jihar Kano: Ammasco, nata sun taimaka wa kanikawa

Tura wannan Sakon

Daga Wakilinmu

Kimanin kanikawan jihar Kano sama da dari ne kamfanin Ammasco da hadin gwiwar kungiyar masu fasahar gyaran ababen hawa na kasa NATA Nigerian Automoble Teachinicial Association suka taimaka wa wadansu ‘yan kungiyar da ke jihar da kayan gyaran mota kyauta, taron ya samu halarta da dama daga cikin ‘yan kungiyar ciki har da mai kamfanin AMMASCO, Alhaji Mustapha Ado, da shugaban kungiyar NATA, Injiniya Dakta Magaji Muhammad Sani.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Injiniya Dokta Magaji Muhammad Sani, da farko ya nuna matukar farin cikinsa a kan yadda shugaban AMMASCO ya amince a taimaka wa ‘yan kungiyar a jihar dama kasa baki daya.

Kwamared Magaji Muhammad Sani, ya bayar da misali da yadda Alhaji Mustapha Ado ya sayi buhunan shinkafa na Naira miliyan 30 domin rarrabawa ‘yan ungiyar a lokacin kullen zaman gida sakamakon annobar Korona.

Alhaji Magaji ya ce, za su ci gaba da tallata kayan  da AMMASCO ke samarwa a jihar Kano da kasa baki daya da yardar Allah, saboda a iya binciken da suka yi man da yake samarwa yana daya daga cikin masu kyau da inganci a fadin kasar nan.

 Sannan kuma har ila yau yana daya daga cikin mutanen  da AMMASCO ya gayyata zuwa Ingila domin ganin yadda ake hada bakin mai.

Daga karshe, Malam Magaji Muhammad Sani, ya kuma sake gode wa Alhaji Mustapha Ado a kan tallafa wa kungiyar da kudi Naira miliyan 3 kyauta domin tallafa wa ‘yan kungiyar da ke jihar a lokacin rarraba kayan tallafin, wannan abu da yake yi wa NATA ba za su manta da shi ba za su ci gaba da ba shi hadin kai da goyon baya.

Da yake gabatar da nasa jawabin shugaban kamfanin ya nuna farin cikinsa a kan hadin kai da goyon baya da kungiyar NATA ke ba su ya ce, wannan nasara ce babba da kamfanin ba zai manta da shi ba, zuwa yanzu ya tabbatar da cewa, AMMASCO ba shi da wadansu abokan hulda na gaskiya da suka wuce kungiyar.

Mustapha Ado ya tabbatar da cewa, taimaka wa ‘yan kungiyar da kayan gyara nan gaba kadan, daukacin ‘yan kungiyar da ke fadin kasar nan za su samu da yardar Allah babban abin da yake bukata daga gurin su, addu’ar fatan alhairi da kuma hadin kai da goyon baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *