A Jihar Kano: APC tana cikin yanayi mai gamsarwa -Inji Ado Tambai

Tambai Kwa

Tambai Kwa

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa ya bayyana cewa, jam’iyyar APC tana cikin yanayi mai kyau a jihar Kano bisa yadda gwamna Dokta Abdullah Umar Ganduje yake kokari wajen bunkasa ta.

Ado Tambai kwa ya yi tsokacin ne a ganawar su da wakilinmu, inda ya sanar da cewa, jam’iyyar APC a jihar Kano tana kara karfi da bunkasa duba da yadda gwamna Ganduje da dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka hada hannu wajen kawo ci gaba mai kyau gareta kuma a matakai daban-daban.

Ya ce, suna gamsuwa da yadda jam’iyyar ta APC take kara samun nasara wajen gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar Kano bisa la’akari da bukatun kowane bangare, wanda hakan ya nunar da cewa, da yardar Allah APC za ta lashe zabubbukan shekarar 2023 da gagarumin rinjaye.

Alhaji Ado Tambai Kwa ya gode wa gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatinsa saboda namijin kokarin da ake yi wajen inganta raguwar al’umma da samar da ayyukan raya kasa a birni da kuma yankunan karkara bisa tsari da sanin ya kamata ta yadda kowa zai amfana da romon dimokuradiyya mai kyau.

Shugaban karamar hukumar ya yi amfani da wannan dama wajen taya shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas murnar kaddamar da shi da aka yi a matsayin halattaccen shugaban jam’iyyar a jihar Kano, tare da jaddada cewa, za su ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa domin samar da ingantaccen ci gaba a fadin yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *